An kirkiro na’urar da zai hana namijin sauro yi wa macen sauro ciki

0

Hukumar ‘International Atomic Energy Agency (IAEA)’ ta hada hannu da kamfanin ‘We Robotics’ inda suka kirkiro wata na’ura mai tashi sama dake tuka kanta da ake kira ‘Drone’ domin yaki da sauro ta hanyar yin feshi da zai kashe karfin Iya yi wa matan sauro ciki.

Jami’in kamfanin IAEA Jeremy Bouyer ya bayyana cewa na’urar za ta taimaka wajen kawar da zazzabin cizon sauro ne ta hanyar yi wa mazajen sauro feshin magani mai suna ‘Sterile Insect Technique (SIT)’wanda zai hana su haihuwa koda sun sadu da matan sauro.

” Hakan zai hana matan sauro da sune ke dauke da kayoyin cutar dake haifar da zazzabi haihuwa.”

A karshe Jeremy Bouyer ya ce sun kirkiro wannan na’ura ne a kasar Brazil sannan bayan an tabbatar da ingancin na’urar za su fara amfani da ita a watan Janairu 2019.

Share.

game da Author