A safiyar Larabar wannan maklon ne tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Na’Abba ya rasu, Najeriya ta yi rashin mai rajin tabbatar da mulkin dimokuradiyya da ‘yancin cin gashin kan ‘yan majalisa.
Marigayi Na’Abba ya rasu a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya. Yana da shekaru 65 a duniya.
An yi jana’izar marigayin a Kano, mahaifarsa a ranar. Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, gwamnoni da sauran manyan mutane ne suka halarci jana’izar.
An haifi marigayi Na’Abba ga iyalan Umar Na’Abba a unguwar Tudun Wada a cikin birnin Kano. Ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, inda ya kamala karatun kimiyyar siyasa a shekarar 1979.
Bayan dawowar dimukuradiyya a jamhuriya ta hudu a shekarar 1999 ya shiga jam’iyyar PDP,inda a wannan jam’iyya ce aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kano Municipal Federal Constituency.
Jim kadan bayan rantsar da sabbin ‘yan majalisar sai shugaban majalisar a wancan lokaci Ibrahim Salisu Buhari ya nada shi shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar.
Amma jim kadan bayan haka, sai Na’abba ya zama kakakin majalisar bayan murabus din da Buhari ya yi saboda samun sa da aka yi da shirga karya ka shekarun sa da ya yi amfani da shi ya zama dan majalisa.
Tun bayan zaman sa shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Na’abba ya saka kafar wando daya da shugaban kasa a wancan lokaci, Olusegun Obasanjo.
Ya fara samun matsala da bangaraen zartaswa ne bayan ya lura cewa bangaren gwamnati na kokarin yafe wa Salisu Buhari laifin da ya aikata kuma ga dukkan alamu akwai yiwuwar zai iya dawowa majalisar ya koma kujerar sa ta kakakin majalaisar tarayya.
Hakan ya sa Na’abba ya falle takobin sa ya ja daga, ya ce sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi.
Daga nan dai sai aka fara takun saka tsakanin shugaba Obasanjo da Na’abba, da a lokacin aka yi kokarin kala masa zargin cewa wai ya yi sama da fadi da wasu kudade na kwangilar siyan Komfutoci wa ‘yan majalisan.
Wasu ‘yan majalisa suka yi kokarin tsige shi daga kakakin majalisar.
Daga nan sai Na’abba tare da mataimakin sa Chibudum Nwoche suka hada kai suka rike wuta, suka rika surfar bangaren zartarswa aka ci gaba da zaman doya da manja tsakanin Obasanjo da Na’abba.
Tun daga wannan lokacin Na’abba bai sake ido hudu da Obasanjo ba har sai da wadin mulkin wannan gwamnati na farko ya zo karshe.
A haka dai aka yi batakashi tsakanin Na’abba da Obasanjo da wasu ‘yan majalisa dake wa bangaren zartas wa aiki a majalisar da kuma tsallake turaku da aka rika dana masa don a tsige shi daga shugabancin majalaisar dattawan.
A cikin wata hudu kacal da zama kakakin majalaisar wakilai ta tarayya, Na’abba ya zama Zaki, shi kadai ya tunkari tsohon janar a soja, tsohon shugaban kasa, kuma shugaban kasa a lokacin ya kuma taka mai burki, ya hana shi sakat, ya kuma tilasta shi dole a bi doka da oda a wurin gudanar da mulkin kasa.
Hakan ya sa aka yi masa da lakabi da “Zaki” yayin da mataimakinsa, Nwuche, ake yiwa lakabi da “Damisa.”
Wani hanya da Na’abba ya yi amfani da shi wajen samun goyon bayan ‘yan majalisa shine ta hanyar canja shugabannin kwamitocin majalisar akai-akai sannan kuma ya yi wa mammbobi kyautattuka akai akai.
Yadda Marigayi Na’abba ya tsalle kutunguilar tsige shi sau 40 cikin wata hudu a matajalisar Tarayya
Misali, a ranar 22 ga Oktoba, 2002, wata kungiyar ‘yan majalisa karkashin jagorancin West Idahosa da ke da goyon bayan bangaren zartaswa, ta kulla makarkashiyar tsige shi.
A wannan rana, ‘Yan Majalisan sun dira majalisa suna jiran Na’abba ya shigo su tsige shi, sai ya ki halartar zaman majalisar sai can da yamma, bayan kowa ya gaji an fusata. Da ga shigowan sa majalisa bayan ya zauna a kujerar sa sai ya tsige duka gaggan yan majalisan da suka nemi tsige shi daga kwamitocin su ya bayyana sabbin yan majalisa da suka maye gurbin su.
Bayan haka kuma, Na’abba ya yi gaba da gaba da Obasanjo inda wasu ‘yan majalisa suka mika takardar gayyatar Obasanjo ya bayyana gaban majalisa domin yin bayani akan wasu korafe-korafe da ake zargin sa da su ko kuma ya fuskanci tsigewa.
Duk da matsalolin da ka fuskanta a majalisar, Na’abba ya samu nasarorin ma su dimbin yawa a zamanin ya na Kakakin majalisar tarayya daga 1999-2003.
Yadda Obasanjo, Atiku, Kwankwaso suka yi wa Na’abba taron dangi a 2003
Sai dai kuma ba kullum a ke kwana a gado ba, Na’abba ya kasa tsallake tuggun da Obasanjo da makarraban sa suka shirya masa tun daga gida Kano har zuwa Abuja.
Da farko dai an ingiza dan tsohon shugaban Najeriya, Janar Murtala MOhammaed ya yi takarar kujerar Na’abba, amma daga karshe ya janye daga takarar.
Bayan haka, a jihar Kano, shima Kwankwaso wanda gwamna ne a lokacin ya ja daga da Na’abba, shima baya son takararsa dan majalisa. Daganan dai Obasanjo da Kwankwaso suka yi wa Na’abba taron dangi sai da suka kada shi da karfin tsiya a zaben 2003.
Tun daga lokacin, siyasa ta ki Na’abba, duk inda ya bi sai ya samu cikas, Ya koma ACN, ya dawo PDP, ya koma ANPP, duk dai kiwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Allah ya ji kan Na’abba, Dimokuradiyya ba za ta manta da irin gudunmawar da ya bada ba a tsawon shekarun da ya yi yana shugabantar majalisar wakilai ta tarayya.
Discussion about this post