Isra’ila tana neman jefa tsarin tattalin arzikin Falasɗin cin tasku, ta hanyar ƙin bayar da cikakken kuɗaɗen haraji ga Falasɗin, a tsawon watanni biyu masu biye da juna; saboda tana son ne ta ba su wani sashe na kuɗaɗen ba duka ba, ma’ana wai bayan ta zaftare rabon da ake bai wa yankin zirin Gaza daga ciki.
A wata sanarwa wacce ke dauke da sa hannu ofishin jakadancin Falasdin dake Abuja, Najeriya, an gano cewa a ci gaba da muzgunawa Falastin da Israila ke yi, ta na yin karfa-karfa wajen zaftare kudaden shiga na haraji da falasdin ke samu a duk lokacin da aka shigo da kaya wannan yanki.
Sanarwar
Muna son mu bayyana cewa: kasancewar Isra’ila ita ce take mulkin mallaka, kuma ita ce take da iko a mashiga Falasɗin a dukan iyakokinta, haka ya sanya dole Falasɗinawa su shigo da kayayyaki, su kuma fitar da kayyaki, a ƙarƙashin ikon Isra’ila kaɗai, akwai harajin da ake biya akan kayayyakin da ake shigo da su zuwa Falasɗin, wanda ɓangaren Isra’ila take amsa, da zaran kayayyakin sun iso kan iyakoki, sannan ta bai wa hukumar Falasɗin, bayan ta cire kashi 3% daga ciki, a matsayin kuɗaɗen gudanarwa a kowane wata, da waɗannan kuɗaɗen ne ake biyan albashin ma’aikatan gwamnati a West Bank da yanki Gaza, haka ma da su ne gwamnatin Falasɗinawa take gudanar da al’amurranta.
Shi karɓan haraji a wurin Falasɗinawa masu shigo da kayayyaki, da miƙa kuɗaɗen ga Falasɗinawa abu ne da da yake rubuce a cikin yarjejeniyoyin da ɓangarori biyun suka rattaba hannu akansu.
Tun lokacin da Isra’ila ta fara ayyukan ta’addancinta, na baya- bayan nan akan Falasɗinawa, musamman a yankin Gaza, Isra’ila ta dage akan cewa sai dai ta tura kuɗaɗen da gwamnatin Falasɗin za ta iya gudanar da al’amurran west Bank kawai, wannan ya zo a cikin azabtawar da take yi wa ɗaukacin mutanen yankin zirin Gaza, da kuma ƙara tabbatar da raba tsakanin Gaza da west Bank da take yi.
Shugaba Mahmud Abbas ya ƙi yarda ya karɓi waɗannan kuɗaɗen daga wurin Isra’ila a tauye, bayan ta zaftare kason da ake gudanar da yankin zirin Gaza, har zuwa yanzu, watanni biyu kenan, gwamnatin mulkin mallaka ta ƙi ta bai wa Falasɗin cikakken kuɗaɗenta, abin da ya sanya gwamnatin Falasɗin ta gaza biyan cikakken albashin ma’aikata a west Bank da zirin Gaza a watanni biyu a jere, hakan ya sanya dole ta ciyo basussuka daga bankunan cikin gida, saboda ta cika ta biya albashin ma’aikata a west Bank da Gaza na watan Oktoban da ya gabata.
Bugu da ƙari, idan muka yi la’akari da matsalolin da suke faruwa a yankin zirin Gaza, za mu fahimci cewa: lallai rashin sakin waɗannan kuɗaɗen haraji, da kuma gaza biyan albashi, da kuɗaɗen gudanarwa abubuwa ne da za su ƙara jefa Falasɗinawa cikin ƙasan talauci, hakan kuma yana kawo cikas wajen gudanar da ayyukan gwamnati, musamman a fagagen lafiya da ilimi, wannan ma abu ne da zai ƙara sanya al’amurra su taɓarɓare a Falasɗin.
Discussion about this post