Kisan Musulamai masu halartar taron Maulidi su 85, tare da jikkata mutum fiye da ɗari wanda Sojojin Najeriya su ka yi a bisa ‘tsautsayi’, ba shi ne na farko ba.
Kisan wanda aka yi a ƙauyen Tudun Biri cikin Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Katsina, ya tada hankulan jama’a da dama. Kuma ana ta kira ga Sojojin Najeriya da Gwamnatin Najeriya cewa a yi bincike, a hukunta sojojin da suka jefa bamabaman, a kuma biya diyyar waɗanda aka kashe da waɗanda aka jikkata.
Jihar Nassarawa: Farar Hula Sama Da 40:
Cikin Janairu 2023 an kai irin wannan hari kan jirgin da ba matuƙi a Jihar Nassarawa, har aka kashe makiyaya 27.
Amma dai Fulani makiyaya sun ce waɗanda aka kashe ɗin sun kai 40.
Waɗanda aka kashe ɗin dai Fulani ne waɗanda ke kan hanyar su ta komawa ruga, bayan sun karɓo shanun su da Gwamnatin Jihar Benuwai ta kama.
Jihar Zamfara: Farar Hula Sama Da 70
Irin wannan mummunan hari kan farar hula ya faru a Jihar Zamfara, a cikin 2022, a cikin yankin Ɗansadau da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maru.
Sojoji sun kai farmakin kakkaɓe ‘yan bindiga a ƙauyen Matunji, sai dai kuma bam ɗin da aka jefa ta sama jirgin yaƙi, ya yi kisan kai-mai-uwa-da-wabi, domin an kashe farar hula sama da 70.
Katsina: Farar Hula 6:
Cikin Yuli, 2022 aka kashe mutum 6 a yankin Kunkunna, cikin Ƙaramar Hukumar Safana. Sojojin Sama ne suka jefa bam dagakam Jirgin Yaƙi samfurin Jet.
Jihar Neja: Yara Ƙanana 6:
Cikin Afrilu 2022, Sojojin Sama sun kashe yara shida masu ɗibar ruwa a rijiyar tsakiyar ƙauyen Kurebe, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro.
Abin takaici, ‘yan bindiga ne suka kashe iyayen yaran da Sojojin Saman Najeriya suka jefa wa bam a cikin 2020.
Jirar Barno: Kisan ‘Yan Gudun Hijira 52:
Cikin watan Janairu, 2017, Sojojin Sama sun jefa bam a Sansanin Masu Gudun Hijira a ƙauyen Rann, suka kashe mutum 52, suka raunata 120. Ƙauyen Rann ya na cikin Ƙaramar Hukumar Kala-Balge a Jihar Barno.
Tun daga kisan na 2017, har zuwa yau, duk da ana cewa a yi bincike, amma har yau shiru ka ke ji.
PREMIUM TIMES ta kira wayar Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, bai ɗauka ba. An tura masa tes shi ma bai maido amsa ba, ballantana a yi halin da ake ciki, dangane da binciken kashe-kashen da sojoji suka ce za su yi a baya.
Discussion about this post