Gwamnatin tarayya na kashe akalla Naira biliyan 2.7 don daukar nauyin wakilan da suka halarci taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya, na sauyin yanayi COP28, wanda aka fara a Dubai a ranar Alhamis din da ta gabata kuma zai ci gaba har zuwa 12 ga Disamba.
Najeriya dai ta aika da wakilai 1,411 sannan kuma ita ce a matsayin na uku da mafi yawan wakilai a taron. Ƙasar mai masaukin baki UAE na da wakilai (4,409) da Brazil mai wakilai (3,081) ne kawai ke da yawan mahalarta fiye da Najeriya da ta fi yawan jama’a a Afirka.
Sauran tawagogin da suka zarce 1,000 sun hada da kasar China da ta yiwa mutane 1,411 rijista kamar Najeriya, sai Indonesiya mai 1,229, Japan mai 1,067 sai Turkiyya mai 1,045.
‘Yan Najeriya da yawancinsu ke rayuwar hannu baka hannu kwarya, sun fusata da yawan manyan tawagogin gwamnati da suka halarci taron a daidai lokacin da hauhawar farashin kayayyakin abinci ya karu da kashi 27.33 cikin 100, kuma a daidai gwamnati na shirin karbo rancen kudi na naira tiriliyan 27.5 da zai cike gibin kasafin kudi na shekarar 2024.
Minista Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki nauyin mutum 422 ne kacal wanda PREMIUM TIMES tabi daki-daki domin fayyace nawa gwamnati ta kashe a wannan tafiya na mutum 412.
An kashe akalla naira miliyan N824 wajen biyan kudin jirgin wadanda suka halarci taron, zuwa da dawowa. Bincike ya nuna cewa akwai wasu jami’an gwamnati da suka bi jirgin yawo zuwa taron.
Kudin Kashewa kawai da aka ba ministocin da suka halarci taron ya tashi akan naira miliyan N248.
Gwamnatin tarayyan ta dauki nauyin yan majalisar kasa 40 zuwa taron. Suma a jimla an kashe musu naira N381
Masu ba shugaban kasa shawara na musamman 13. Suma an kashe musu naira miliyan N110.
Manyan darektocin 14 da suka halarci taron suma an kashe musu naira miliayn N74.
Baya ga haka, akwai manyan sakatarori, jakadai, jami’an gwamnati da suma sun shiga cikin wannan watandar biliyoyi da gwamantti ta yi.
A Afirka, Maroko ta aika da tawaga ta mutane 823 zuwa Dubai, Kenya, 765; Tanzaniya 763, Ghana, 618.
Discussion about this post