Yadda sojoji suka cafke gogarman masu garkuwa da mutane da wasu 150 a dazukan Zamfara da Katsina

0

Dakarun sojin Najeriya dake karkashin rundunar ‘Operation Sahel Sanity’ sun kama maharan da suka buwayi mutane a jihohin Katsina da Zamfara.

Mataimakin Shugaban yada labarai na rundunar Benard Onyeuko ya sanar da haka wa namena labarai a sansanin jami’an tsaron dake Faskari jihar Katsina ranar Talata.

Onyeuko ya ce dakarun sojin sun kama wasu mahara 150 da makamai 120 a Wani wurin da ake hako ma’adanai ba tare da izini ba a karamar hukumar Bukuyun, jihar Zamfara.

Onyeuko ya kara da cewa jami’an tsaron sun dira maboyar mahara dake karamar hukumar Anka, jihar Zamfara inda suka kama mahara uku, bindigogi biyu, gidajen harsashi biyu da baburan hawa.

“A kauyen Daki Takwas dake karamar hukumar Gumi dakarun sun kama wata mota kirar Toyota dauke da bindigogi da aka boye su a motar.

” Haka kuma a kauyen Dogon Karfe a karamar hukumar Bakura a kama wani kasurgumin dan fashi mai suna Yusuf Ibrahim Wanda aka Fi sani da Bula sannan sun yi fata-fata da maboyar.

“Dakarun sun Kuma Kama babbar mota dankare da shannun sata a hanyar Gurbi-Jibia dake jihar Zamfara Kuma sun kama wasu mahara guda biyu Mas’udu Abubakar da Tukur Halliru a kauyen Daudawa dake karamar hukumar Faskari jihar Katsina.

Onyeuko ya ce rundunar sojin Najeriya ta danka wadannan mahara hannun ‘yan sandan jihar Zamfara domin gudanar da bincike.

Share.

game da Author