Wani binciken da aka gudanar a kasashe 85, ya tababtar da cewa Najeriya na sahun gaban kasashen da aka fi amfani da intanet da tsadar tsiya.
Wani kamfanin Amurka mai suna Surfshark Press, ya fitar da rahoton binciken da ya yi cewa ko Colombia da Honduras ba su kai Najeriya shan intanet da bala’in tsada ba.
“Najeriya aka fi tsadar intanet a duniya. Ko Columbia da Hunduras ba su kai Najeriya tsadar intanet ba.” Inji rahoton.
Kamfanin ya ce a nazarin da suka yi, kowace kasa su na auna mafi arhar waya da kuma irin tsarin intanet da ‘data’ din da ake amfani da su a kasar.
A kididdigar da aka fitar, Najeriyace ta 81 a cikin kasashe 85.
An yi binciken a bisa sikeli guda biyar: Saukin mallakar intanet; karfin intanet; kayan amfani da intanet; sahihancin kayan sadarwa masu amfani da lantarki..
Wadannan kasashen da aka yi bincike a cikin su, su na da jimillar yawan al’umma bilyan 6.3.
Kasashen da aka yi nazari a Afrika sun hada da Afrika ta Kudu, Kenya, Morocco da Tunisia. Kuma wadannan kasashen hudu duk sun fi Najeriya saukin wadata da arhar intanet.
Kasar Aljeriya ce kadai ke bi bayan Najeriya, inda ita ce ta 84 a duniya. Afrika ta Kudu ce ta 59, Kenya ta 77, Morocco ta 70 sai Tunisia ta 64.
Sai dai kuma Najeriya ta dan cirza wajen tsarin kiyaye laifuka ta hanyar intanet, wato ‘cybersecurity’, inda ta zo ta 53.
Najeriya na da ingancin karfin intanet fiye da kasahen Peru, Aljeriya, Phillippines da kuma Sri Lanka.
Wace Kasa Ta Fi Ingancin Intanet a Duniya?
Kasar Denmark ce ta fi kowace kasa, sai Sweden, Canada, France, Norway, Netherlands da Birtaniya.
Amurka ce ta 22, Chana ta 38, sai Rasha ta 42. Sannan akwai sauki a kasashen Isra’ila, Canada, Azerbaijan, kamar yadda rahoton ya nuna.