Tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya fito a yau Laraba ya nemi afuwar cin mutuncin da ya yi wa wakilin jaridar Daily Trust da ke Calabar, babban birnin Cross River.
Cikin shafin sa na Twitter, Fani-Kayode ya nemi afuwar Eyo Charles, inda a cikin shafin ya bayyana cewa, “Na gana da mashawarta na, kuna ina so na sanar cewa na janye wannan kalma ta “mutumin banza” da na kira Charles, a taron manema labarai a Calabar.”
“Ina da abokai da dama a da’irar masu aikin jarida, wadanda na bata wa rai, saboda giyar fushin da ta fizge ni har na yi sakin-bakin yin mummunan kalamin da bai dace ba. Ina mai nadamar abin da na aikata.”
Sai dai kuma Femi ya ce bai yi wa Dan jaridar wata barazana ba, kuma bai tura wani ya yi masa barazana ba.
“Duk wanda ya fadi haka, to karya ya yi min. Kuma ina kalubakantar sa da ya gabatar da hujja.”
Femi ya ce tsawon shekaru talatin ya na hulda da ‘yan jarida, kuma bai taba ji wa wani ciwo ko barazanar lahanta wani ba.
Ya ce ya na bada hakuri ga duk wanda ran sa ya sosu, saboda bambarmar da ya aikata.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin irin bambarmar da Femi ya yi, inda a raanr Talata ta bada labarin cewa dan jaridar da Femi Fani-Kayode ya ci ws mutunci ya bayyana halin takaicin da ya shiga
Wakilin jaridar Daily Trust na Jihar Cross River da tsohon minista, Femi Fani-Kayode ya ci wa mutunci a zauren taron ‘yan jarida a Kalaba, ya bayyana wa PREMIUM TIMES irin tozartawar da Femi din ya yi masa.
An dai nuno wani bidiyo inda Fani-Kayode ke tashi a fusace ya fice daga dakin taron manema labarai, bayan ya yi wa Eyo Charles, wakilin Daily Trust a Kalaba.
Kayode ya ce wakilin Daily Trust ys yi masa tambayar rashin kunya, rashin ganin girman sa da kuma tambayar tozarta shi a idon duniya.
Lamarin ya faru a ranar Alhamis a wani otal a Kalaba, inda tsohon Ministan ya tara ‘yan jarida domin yi masu karin bayanin rangadin da ya ke yi a jihohin Kudu maso Kudu.
Tambayar Wakilin Daily Trust Da Ta Harzuka Femi Fani-Kayode:
Tambaya: Wakilin Daily Trust ya nemi sanin ko akwai wanda ke daukar rangadin da Femi ke yi a jihohin da ya yi karakaina.
Femi: “Wace irin tambayar banza da wofi ce ka ke yi min? Wa ke daukar nauyin wa? Ni ake daukar nauyi na? Shin ka kuwa san da wanda ka ke magana kuwa?” Inji Femi Fani-Kayode a fusace.
Daga nan ya waiwaya ya kalli kakakin yada labarai na Gwamna Ayade, wanda ke zaune kusa da shi, ya ce ba zai sake amsa wata tambaya daga bakin Charles ba.
Daga nan kakakin yada labarai Its ya rika ba shi hakuri, ya na cewa, “hucewa yallabai”, amma dai Femi Fani-Kayode bai hakura ba.
“Na lura da fuskar ka tun ma kafin a shigo zauren taron nan, kai mutumin banza ne. Kada is sake yi min irin wannan zancen wofin.”
Wakilin Daily Trust dai na tsaye, bai sake cewa komai ba. Sai da Femi Fani-Kayode ya gama surfa masa zagi, sannan ya ce buda baki ya ce masa, “hucewa yallabai.”
Kamar ya kara hura wa Femi Fani-Kayode wuta, sai tsohon ministan ya sake cewa, “kada ka dauka daidai na ke da shashasha irin ka. Tun cikin 1990 na shiga siyasa. Babu irin gwagwarmaya da daurin da ba a yi min ba. Ba kamar irin ‘yan siyasar da ku ke bi ku na yi musu maula ba.
“Ni ba matsiyaci ba ne. Ba na rokon wani ya ba ni kudi. Ban taba roko ba, kuma ba zan taba rokon kowa ba.”
Daga nan babu wanda ya kara yi masa wata tambaya, sai ya tashi ya fice a fusace.
“Ya shamamce ni” -Wakilin Daily Trust
Charles ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Fani Kayode ya shammace shi, ya rasa ma yadda zai yi, shi ya sa kawai ya ce masa ya yi hakuri.
Sai dai kuma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ‘yan jarida sun rika cewa bai kamata ya yi masa irin tambayar da ya yi masa din ba.
Ya ce bai yi tsammanin Femi Fani-Kayode zai hau shi da hargagi da zage-zage irin na ‘yan jagaliya ba.
“Ni fa tambayar sa na yi cewa: Yallabai ka ce ka yi rangadin jihohi shida ko bakwai. Yanzu ga shi ka kammala rangadin ka a Cross River ka ga ayyukan da wadannan gwamnoni suka yi. Shin wa ke daukar nauyin wannan rangadi da ka yi?”
Ya ce bayan taro ya watse ba shiri, wani jami’in tsaron Femi Fani-Kayode ya same shi ya rika yi masa wasu tambayoyi. Da ya ga haka, sai ya yi sauri ya bar wurin.
Femi Fani-Kayode Ya Nemi A Kore Ni Daga Aiki:
Charles ya ce daga baya tsohon ministan ya kira Editan Daily Trust, ya nemi a kore shi.
Kakakin gwamnan Cross River, Ita, ya ce tambayar rainin hankali aka yi wa Femi, shi ya sa ya harzuka.
Charles ya ce ya yi nadamar hakurin da ya ba Femi Fani-Kayode.
“Shekaru na 53 a duniya. Bai girme ni sosai ba fa. Kuma ni ma ina da iyali. Da na sani da ban ba shi hakuri ba.”