Alkaluman Korona na ranar Sallah: Abuja 93, Filato 64, Kaduna 54, yanzu 43,151 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 462 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 79, FCT-93, Filato-64, Kaduna-54, Oyo-47, Ondo-32, Adamawa-23, Bauchi-19, Rivers-9, Ogun-9, Delta-9, Edo-7, Kano-6, Enugu-6, Nasarawa-5 da Osun-1.

Yanzu mutum 43,151 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 19,565 sun warke, 879 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,707 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,121 FCT – 3,803, Oyo – 2,760, Edo – 2,292, Delta – 1,510, Rivers 1,791, Kano –1,597 , Ogun – 1,394, Kaduna – 1,457, Katsina –742, Ondo – 1,155 , Borno –613, Gombe – 607, Bauchi – 560, Ebonyi – 785, Filato – 1,188, Enugu – 807, Abia – 545, Imo – 468, Jigawa – 322, Kwara – 753, Bayelsa – 328, Nasarawa – 317, Osun – 524, Sokoto – 153, Niger – 224, Akwa Ibom – 221, Benue – 346, Adamawa – 163, Anambra – 135, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 132, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 45.

KIRA GA MATASA: Cutar Korona har kisa ta na yi idan ta Kama matashi – Shugaban WHO

Shugaban Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus ya gargadi matasa da ke cewa kwayoyin cutar Korona ba zai iya kama su ba da su daina wannan zato, yana mai cewa ba kama matashi ba ma kawai har kisan sa zai iya yi idan bai kiyaye ba.

Bayan haka kuma ya shaida cewa lokaci yayi da kasashen duniya za su koyi shirin zama dindindin da kwayoyin cutar Korona.

Dole ne mu koyi rayuwa da wannan cuta tare da ɗaukar matakai domin mu rayu, tare da kare kanmu da sauran jama’a.

Sannan kuma ya yabawa kasar Saudiyya kan irin matakan da ta ɗauka yayin gudanar da Aikin Hajjin bana.

Share.

game da Author