BABBAN SALLAH: Ga dai raguna, babu masu siya a Kaduna

0

Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA, ya zazzagaya wasu daga cikin manyan kasuwannin saida raguna a Kaduna ranar Sallah inda ya gano halin da ‘yan kasuwa ke ciki a wannan yanayi da mutane ke kuka da rashin kudi a dalilin annobar Korona.

Kasuwar da aka fara dira kuwa itace kasuwar ‘Yan Awaki dake Kawo, Kaduna.

Ko da Wakilin mu ya isa wannan Kasuwa sai ya iske tulin raguna daddaura a turakun su, su kuma masu saida su suna zaune zugudum suna jiran masu siya su bullo.

Wani daga cikin mai saida dabbobi a wannan kasuwa, Mal Umaru Mai-Rago ya koka cewa rashin kudade a hannun mutane ne babban dalilin da ya sa ake kwantai da raguna suka yi a Kaduna.

” Ka duba ka gani ko ina ka juya za ka ga rago. Kamar ba a yi Layya ba. Ko da yake an saida raguna amma kuma duk da haka ga raguna kamar ba a saida su ba. Mutane sun koka kan rashin kudi a hannun su.

” Muna sa ran cewa tunda ana yin layya har zuwa jibi, akwai yiwuwar wasu su garzayo su sayi rago. Sai dai kuma tabbas dole farashin ragunan su karya domin wasu da dama zuwa da su suka yi daga wasu jihohin.”

Masu saida ragunan sun shida cewa ko wajen dakon ragunan daga wasu jihohin zuwa Kaduna sai ka biya wa kowanni rago daya naira 1000. Maimakon ka maida su gida kasake biya musu kudin mota gara ka karya farashin ka siyar .

Da muka zanta da wani magidanci game da ko menene babban dalilin da yasa aka samu karancin masu siyan rago a wannan shekara, ya ce ” Korona ce babban dalilin da ya sa mutane suka hakura da layya bana. An kori wasu daga aikin saboda Korona, an dakatar da wasu saboda Korana, Wasu ba albashi tun daga Maris da aka rufe Kasa, sannan kuma ga tsadar Abinci, da wanne za aji.”

Masu saida raguna sun ce har yanzu suna sa ransa masu layya za su ci gaba da zuwa har zuwa karshen ranar da aka kebe domin yin layya din.

Wannan matsala dai ita ce aka iske a Kasuwar Dabbobi dake Zango, da wasu wuraren da ke saida da dabbabo a fadin jihar.

Share.

game da Author