APC za ta ci gaba da mulki har bayan 2023 – Shugaban Mata

0

Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC, Stella Okotete, ta bayyana cewa ta na jin alamomi a jikin ta cewa APC za ta ci gaba da mulki a Najeriya, har bayan shekarar 2023.

Okotete ta yi wannan kalami ranar Juma’a a lokacin da ta jagoranci tawagar da ta kai wa masu gudun hijira abinci, a sansanin da ke Karmajiji, kusa da Abuja.

“Kokarin da mu ke a kai na yi wa APC garambawul ya na haifar da alheri. Ga shi kuma sai sabbin mambobi ke kara yin tururuwa su na shiga APC, tsoffin da suka tafi a baya suka bar jam’iyyar, sai dawowa suke yi.”

Don haka ne ta ce ta duba yiwuwar APC ta ci gaba da mulki har bayan 2023.

“Zan iya shaida muku cewa jihohin da ba APC ke mulki ba duk za su dawo a hannun mu nan da zaben 2023. Amma daga Jihar Edo za mu fara karba daga hannun PDP kwanan nan.

“Za mu sake dawo da Jihar Edo a hannun APC, haka Anambra, kuma haka abin zai tafi har sauran jihohin su dawo hannun APC ” Inji shugabar matan ta Jam’iyyar APC.

Ta kara da cewa jam’iyyar APC a karkashin rikon Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe, a cikin wata daya ya farfado da jam’iyyar, ta kara saisaita kuma ta kara daidaita sahu.

Okotete ta ce ta jagoranci tawagar zuwa sansanin ne domin tallafawa ga nskasassu da jawarawa ko wadanda suka rasa mazan su da buhunan wake, na shinkafa, katan-katan na Indomie, man girki, garin kwaki da sauran kayan abinci da na masarufi.

Ta sha alwashin cewa duk da dai masu bukatar kayan agaji na da yawa, to ba za a ci gaba da taimaka musu.

Ta ce gwamnatin Buhari za ta gaggauta ganin sun koma gidajen su ba da dadewa ba.

Share.

game da Author