Mahara sun kashe mutane 30 sun sace sama da 100 a Kaduna

0

A wani abin tashin hankali da fargaba da ya auku a titin Kaduna zuwa Zaria, wasu Mahara dauke da manyan bindigogi sun far wa matocin sarkin Potiskum da wasu matafiya da dama a titin Kaduna zuwa Zaria inda suka kashe akalla mutane 30.

Maharan wadanda aka bayyana cewa suna sanye ne da kayan sojoji sun bude wa motocin sarkin Potiskum wuta ne da misalin karfe 11 na daren ranar Talata.

Abin dai yayi muni don an tabbatar cewa maharan sun arce da mutane akalla 100 a wannan hari yan 30 da suka kashe nan take.

Ssi dai kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa mutane shida ne kawai aka kashe, biyar kuma sun samu rauni. Cikin wadanda suka rasu akwai dogaran sarkin Potiskum din hudu.

Wannan yana daga cikin mummunar hari da aka kai a dan kwanankin nan a jihar Kaduna.

A makon da ta gabata, an yti garkuwa da wasu yara dake Kakau har su hudu. Har yanzu dai ba a sako su ba.

Share.

game da Author