Buhari ya jinjina wa Kotun Koli, bayan kwace kujerar gwamnan Imo daga PDP

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa juriya da karfin-halin da Kotun Koli ta nuna wajen kwace kujerar gwamnan jihar Imo daga hannun gwamna Ihedioha na PDP, ta bai wa Hope Uzodinma na APC.

Dukkan Alkalai bakwai masu zaman hukuncin ne suka amince da a kwace kujerar a bai wa wanda ya zo na hudu, a zaben da aka gudanar na gwamnan jihar Imo a ranar 9 Ga Maris, 2019.

Kotu ta yi biris da yawan kuri’un wanda ya zo na biyu da na uku, ta bai wa na hudu.

Yayin da jam’iyyar PDP ta ce sakamakon hukuncin ya yi zafi kuma bai yi wa jam’iyyar dadi ba ko kadan, shi kuma Buhari da APC cewa suka yi hukuncin ya yi musu dadi sosai.

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin Buhari, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce “hanyar tabbatar da adalci ta na da nisa da kuma wahalar cimmawa, amma a karshe dai gaskiya na yin ranar ta.

Buhari ya kuma taya Uzordinma na APC murnar zaben da aka kwace daga Ihedioha na PDP aka ba shi.

Ita ma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi magana a kan hukuncin da Kotun Koli ta yanke, inda ta tsige gwamna Ihedioha na PDP a Imo ta dora Hope Uzordinma na APC.

Nan take bayan tsige Ihedioha, sai Kotun Koli ta bada umarni ga INEC cewa ta kwace satifiket daga gwamnan ta kekketa, sannan ta gaggauta bayar da sabon satifiket ga Uzordinma.

Kakakin INEC Festus Okoye ya yi bayanin cewa INEC ba ta da wani zabi sai ta amince da hukuncin da Kotun Koli sannan kuma za ta bi dukkan umarnin da kotun ta bayar.

Okoye ya ce da zarar INEC ta samu umarni a rubuce daga Kotun Koli, to za ta gaggauta damka sabon satifiket na shaidar cin zabe ga sabon gwamna Uzodinma.

“Duk hukuncin da Kotun Koli ta zartas, shikenan magana ta kare, babu sauran korafi kowata jayayya.

“INEC ba ta da sauran wani hurumin yin wata magana ko ja-in-ja, ko wata tankiya ga hukuncin da Kotuj Koli ta yanke.

Kotun Koli ta kwace kujerar gwamna daga Ihedioha na PDP ta dora Uzordinma na APC wanda ya zo na hudu.

Wannan hukunci ya zama abin magana a fadin kasar nan, inda kowa ke tofa albarkacin bakin sa.

Yayin da wasu ke makaki, da dama kuma na cewa tunda har Kotun Koli ta rigaya ta yanke hukunci, to ba su da sauran abin cewa, sai dai su ce wata shari’a sai a lahira.

Ranar Litinin Kotun Koli za ta yanke hukuncin zaben gwamnan Jihar Kano, inda Gwamna Abdullahi Ganduje a yanzu haka ke zaman zullumin ko za a iya kwacewa a bai wa Abba Yusuf na PDP.

Idan Kotun Koli ta kara jaddada Ganduje, sai dai Abba ya hakura kenan, ya tari 2023.

Ita ma shari’ar karar Gwamna Sokoto, za a yanke hukuncin ta a ranar Litinin mai zuwa.

Share.

game da Author