DAKARUN AMOTEKUN: Gwamnatin Tarayya ba ta isa hana mu kafa jami’an tsaro ba – Akeredolu

0

Duk da haramta Dakarun Amotekun da jihohin Ondo, Lagos, Oyo, Osun, Oyo, Ogun da Ekiti suka kafa a cewa haramtattu ne, amma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Yamma, Rotimi Akeredolu ya shaida cewa ba za su fasa kafa rundunar ba.

Ya ce gwamnonin yankin su a shirye suke domin su bi kadin tabbatar da cewa kungiyar ta su ta kafu a mataki na shari’a a kotu.

Akeredolu ya yi wannan furuci a wurin Taron Tunawa da ‘Yan Mazan Jiya a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Wannan raddi na sa ya biyo bayan da Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda a shakaranjiya Talata ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta haramta Amotekun.

Yayin da Malami ya ce dokar kasa ba ta amince gwamnonin jihohin Yarbawa su kafa dakarun Amotekun ba, su kuma gwamnonin sun ce sun kafa dakarun ne domin kawar da fitinar mahara, masu garkuwa da mutane da kuma rikice-rikicen makiyaya da manoma a yankunan su.

Akeredolu ya kara yin bayanin cewa Dakarun Amotekun ba wasu dakaru masu dauke da manyan makamai ba ne, sai dai kawai za su rika ayyukan taimakawa ne ga sauran rukunonin jami’an tsaron Najeriya.

Wasu da suka boyi bayan kafa Amotekun tare da yin kakkausar suka ga Gwamnatin Tarayya, sun hada da masanan shari’a Itse Sagay, Mike Ozekhome da Olusola Oke.

Akwai Femi Falana, Farfesa Wole Soyinka, Kungiyar Dattawan Yarbawa, Kungiyar Shugabannin Yankin Middle Belt da wasu da dama.

Sai dai kuma shi tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida mai ritaya, cewa ya yi shirin kafa dakrun mai kyau ne, amma kuma zai fuskacin manyan tangardodi a gaba.

Don haka a cewa Babangida, gara ma kada a kafa dakarun kawai, shi ne mafi muhimmanci.

Share.

game da Author