Adawar siyasar APC da PDP bai hana jigajigan ‘yan siyasar Najeriya amsa gayyatar tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu daurin auren ‘ya’yan sa biyu ba.
An daura auren Mahmood Ribadu a masallacin Annur dake babban birnin tarayya Abuja.
Jigajigan ‘yan siyasar Najeriya da mashahuran attajiran kasar duk sun halarci wannan daurin aure.
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, Bashir Ahmad, gwamnoni da tsoffin gwamnoni duk sun halarci wannan daurin aure.
Baya ga su Aliko Dangote, Otedola duk sun halarci wannan daurin aure.