JAMB ta dakatar da amfani da katin dan kasa lokacin jarabawar 2020

0

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB ta bayyana dakatar da dokar da ta gindaya cewa sai dalibi ya mallaki katin dan kasa kafin a bar shi ya rubuta jarabawar UTME ta 2020.

Shugaban JAMB ishaq Oloyede ne ya bayyana haka a lakacin da ya ke wa manema labarai jawabi a yau Asabar a Abuja.

Ya ce hakan da aka yi zai bai wa daliban su samu isassashen lokacin zuwa domin su mallaki katin su na shaidar dan kasa.

Ya ce an dakatar da shirin ne har ma da dalilin cewa an fuskaci matsaloli a wasu cibiyoyin rubuta jarabawar.

Ya shawarci masu rubuta jarabawa su yi biris da batun amfani da lambar shaidar rajitar katin shaidar dan kasa a jarabawar 2020.

Sai dai kuma ya ce amma tilas za a yi amfani da ita a jarabawar shekarar 2021.

A shekarar da ta gabata ne JAMB ta ce duk wanda zai zauna jarabawar 2020 ta shiga jami’a, to dole sai ya mallaki katin shaidar dan kasa.

A amma kuma a yau JAMB ta bakin shugaban ta, Ishaq Oyolede, ya ce an daga kafa a wannan shekarar, don haka kowa zai iya zaunawa jarabawa, ba tare da mallakar katin ba.

Sai dai kuma ya ce amma tilas sai da katin za a zauna jarabawar a shekarar 2021.

Share.

game da Author