ZAMFARA: Dakarun Najeriya sun kashe mahara sama da 100, sun cafke gogan dillalin bindigogi ‘Kunene’

0

Rundunar tsaro na hadin guiwa da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun kashe maharan da suka ki tuba su ka ki ajiye makamai sama da 100 a dazukan jihohin Zamfara da Katsina.

Kakakin rundunar mayakan Najeriya dake aiki a wadannan yankuna Ayobami Oni-Orisan ya bayyana cewa an samu nasarar fatattaka wadannan mahara ne bayan jami’an tsaro sun afka musu har inda suka boye a dazukan.

” Zuwa yanzu dai dakarun sun fatattaki maharan da ke boye a dazukan dake Tashar Kuturu, Dankalgo, Gobirawa junction, Bagega, Kawaye, Duhuwa, Sabon-Birni, Dankurmi, Dangulbi, Hayin Bawa, Zango, Unguwar Shanu, Tundu Mali, Magazu, Mayanchi da dajin Gando da suke kanannan hukumomin Anka, Talatan Mafara, Tsafe, Maru da Bukkuyum duk a jihar Zamfara.

” Sannan kuma da taimakon sojojin sama da suka rika yi wa dazukan yankin karamar hukumar Jibia man wuta daga sama, mun fatattaki maharan da ke boye a nan kuma mun kashe da dama sannan mun cafke wasu

Bayannan rundunar ta cafke wani kasurgumin dillalin bindigogi da ke safarar su yana saida wa mahara a wadannan dazuka mai suna “Kunene”. Ya ce sun samu nasarar kama shi tare da hadin guiwar sojojin kasar Nijar.

Baya ga shi an kama wasu miyagun mutane da ke cin karen su ba babbaka a wadannan dazuka wajen yin garkuwa da mutane su uku. Wadannan mutane kuwa sune, Abubakar Kiri Koloma, Abubakar Ibrahim da Haruna Alhaji Yaro.

Sannan kuma jami’an tsaron sun damko wasu mutane biyu dake safarar muggan kwayoyi ga wadannan mahara zuwa cikin dazukan. Wadanda aka kama sune Kabiru Abubakar Isah da Hamisu Dan-kwanba.

Share.

game da Author