Cikin 2005, jami’an EFCC sun kai samamen bincike a Jos, babban birnin Jihar Filato da niyyar bankado harkallar makudan kudade, a karkashin gwamnatin lokacin, ta tsohon gwamna Joshua Dariye.
Maimakon su samu hadin kai, sai ‘yan jagaliyar siyasa suka yi musu kofar raggo, ana “ku tare, ku buge.” Ba a bubbuge su ba, amma an bubbuge motoci biyu da jami’an ke ciki. Kuma an raunata wasun su.
Bayan saukar Dariye, EFCC ta maida hankali a kan gurfanar da shi kotu, kuma a karshe sai da ta tabbatar wa Mai Shari’a hujjojin da suka tabbatar da cewa Dariye ya karkatar da makudan kudade. Nan take kotu ta daure shi. A zaman yanzu haka ya na Gidan Kurkukun da ke garin Kuje, kusa da Abuja.
Duk da kiran kan Rabaran da tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame ya ke yi, tsoron Allah a zuciyar sa bai yi karfin da ya hana shi wawurar dukiyar jama’a ba. Haka kuma kasancewar Rabaran bai sa EFCC kauda kai daga harkallar da ya yi ba. Bayan saukar sa gwamna, an shafe shekaru ana faman shari’a a kotu. A karshe shi ma dai ya na can kulle a kurkuku.
Na ukun su shi ne tsohon gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor-Kalu, wanda aka shafe shrkaru 12 cur ana shari’ar sa. A karshe dai ranar Larabar da ta gabata ne Mai Shari’a Mohammed Idris na Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ya gamsu da hujjojin da EFCC ta gabatar cewa Kalu ya karkatar da naira bilyan 7.65.
Zaman yanzu Kalu na Gidan Kurkukun Ikoyi da ke Lagos, ya fara zaman wa’adin daurin shekaru 12.
Shakkun Da Talakawa Ke Wa Wasu Makusantan Buhari
GODSWIL AKPABIO: Kwanaki kadan bayan saukar sa mulkin Jihar Akwa Ibom, cikin 2015, jami’an DSS sun shiga gidan sa kuma sun samu daki dankam da makudan kudade.
Ranar 7 Ga Agusta, 2016 kuma, jaridar PUNCH ta buga labarin cewa, “EFCC za ta kwace kadarorin Akpabio.”
“Mun yi bincike a bankin Zenth da FCMB da UBA. Sannan kuma mun gano wasu manyan gidajen sa a Lagos da Abuja. Nan da dan lokaci kadan za mu kwace wadannan kadarori na sa.” Inji majiyar EFCC ga PUNCH.
Sai dai kuma cukumurdar siyasa ta sa Akpabio ya fice daga PDP, ya koma APC, watanni kadan kafin zaben 2019. Buhari ya yi masa kyakkayawar karba, domin a jihar sa Shugaba Buhari ya fara kamfen na zaben 2019.
Duk da PDP ce ta sake lashe zaben Akwa Ibom, kuma Akpabio ya fadi zaben sanata, sai da Buhari ya nada shi Ministan Harkokin Neja Delta. Bincike da tuhuma kuwa sai an kafa wata gwamnati kenan.
ROTIMI AMAECHI: Bayan lashe zaben Jihar Rivers da Gwamna Wike ya yi cikin 2015 a karkashin PDP, ya kafa kwamitin binciken gwamnatin Rotimi Amaechi, inda aka same shi ko zarge shi da karkatar da sama da naira bilyan 100.
An je kotu, amma Amaechi ya nemi a hana binciken sa da gurfanar da shi. Kotu ta ce sai an bincike shi. Ya daukaka karar hana binciken sa har zuwa Kotun Koli.
Kusan shekaru uku kenan maganar ta na Kotun Koli. Ba a ci gaba da shari’a ko bin ba’asi ba. Ita ma sai an kafa wata sabuwar gwamnati kenan.
ADAM OSHIOMHOLE: Bayan saukar sa gwamnan Jihar Edo, wani dan rajin kare hakkin jama’a ya bututa wa EFCC takarda tare da neman su binciki Oshiomhole. Shi ma sai ya garzaya kotu ya roki kada a binciken shi. A karshe ma sai ya zama Shugaban APC dungurugum.
BOLA TINUBU: Baya ga cewa ya yi fama da EFCC tun lokacin da Nuhu Ribadu ke shugaban hukumar, milyoyin jama’a na ganin EFCC a yanzu dai ba ta kyauta ba, ganin yadda ta kauda kai daga binciken makudan kudaden da Tinubu ya ciki motoci biyu daga banki ya kai gida a ranar jajibirin zabe.
An rika cewa idan ba a binciki Tinubu ba, mene ne fa’idar kama masu raba naira 1000 dai-daya a ranar zabe?
DANJUMA GOJE: Har yau jama’a na ganin cewa siyasa ce ta sa aka soke shari’ar Sanata Danjuma Goje, bayan an shafe kusan shekaru goma ana fafatawa.
Baya ga Goje, jama’a na ta mamakin yadda janyo irin su Timipre Silva, Fayemi, Babachir Lawal da wasu da dama a cikin wannan gwamatin. Ba su kadai kenan ba, akwai wasu da dama da ake wa kallon cewa sun shige cikin malum-malum din Shugaban Kasa.
Wadanda Ake Kafsa Shari’ar Su A Kotu
Akwai su da dama, sai dai kuma akasarin su ‘yan adawa da hammaya ne. Ko da dai akwai na jiki da cikin gwamnati da dama.
Cikin wadanda ake shari’a a yanzu akwai tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, Femi Fani Kayode, Sule Lamido, Ibrahim Shema, Saminu Turaki, Murtala Nyako da sauran su.
TIMIPRE SLYVA: Silva ya yi gwamna a jihar Bayelsa a karkashin jam’iyyar PDP. Cikin 2012 EFCC ta kai masa wata raraka, inda ta rika wace fankama-fankaman gidajen sa a Abuja. Daga cikin rukunin gidajen, har akwai wadanda ke kan titin Thaba Tseka, cikin Wuse 2, wadanda EFCC ta garkame a gaban marubucin wannan bayani.
Daga baya an maida wa Sylva kadarorin sa, ya koma APC jikin Buhari, inda bayan zaben 2019, Buhari ya nada shi Karamin Ministan Ferur.