A kauyen Obosi dake jihar Anambra ne ‘yan sanda suka cafke wani lalataccen faston cocin ‘Mountain On Fire Ministries’ mai suna Chukwudi Chukwumezie wanda aka fi sani da’Agudo Jesus’ da laifin yin lalata da wata ‘yar shekara 15.
An dai gano cewa hakan ba shine na farko ba da wannan fasto ke aikata irin wannan mummnar abu.
Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Anambara Haruna Mohammed ya bayyana cewa a ranar 24 ga watan Satumba mahaifiyar wannan yarinyar ta kawo karar Agudo Jesus ofishin ‘yan sanda vewa yayi lalata da ‘yar ta.
Mahaifiyar wannan yarinya ta shaida mana cewa shi wannan fasto ya garzayo gidanta ne inda ya gaya mata cewa Allah yayi masa wahayin cewa wannan yarinya za ta zama mashahuriyar attajira, sai dai akwai wasu shedanu da suka dabaibaye ta kuma hakan zai iya kawo mata cikas.
Sannan kuma ya ce an yi masa wahayi ya rika biya mata kudin makaranta.
“ Daga nan sai ta mika masa wannan ‘ya na ta. Shi ko gogan naka sai ya rika yin lalata da ita sannan ya na yi mata addu’o’in karya.
” Yarinyar ta bayyana cewa takan bude ido ne ta ganshi resheshe a gado da ita.
Sai dai Agudo Jesus ya musanta aikata abinda ake zarginta da shi. Ya ce sharri ce kawai ake masa.
A karshe Mohammed ya ce sakamakon gwajin likitoci ya tabbatar cewa an yi lalata da wannan yarinya sannan sun samu wasu shaidu kuma daga dakin otel din da Agudo Jesus ya rika lalata da wannan yarinya.
Discussion about this post