Jaruman Kannywood da masoya sun mika ta’aziyyar su ga Hafsat Idris a dalilin rasuwar mahaifinta

0

Dubban masoya da abokan aikin jaruman wasan fina-finan Hausa sun mika ta’a ziyyar su da addu’o’i ga jaruma Hafsat Idris a dalilin rasuwar mahaifinta.

A safiyar Asabar ne jaruma Hafsat ta saka a shafinta ta Instagram cewa Allah yayi wa mahaifinta Alhaji Idris rasuwa.

A hoton an nuno jaruma Hafsat rungume da mahaifinta ta na kuka ta na jimamin rashinsa da suka yi.

Abokan aikinta maza da mata sun yi tururuwa zuwa shafinta domin mika ta’aziyyar su kan wannan rashi da jarumar tayi.

Fitaccen dan wasa kuma jarumi a harkar fina-finan Hausa, Nuhu Abdullahi a sakon ta’aziyyar sa ya roki Allah ya gafarta wa mahaifin jaruma Hafsat, yasa Aljanna ta zamo makomar sa.

Usman Uzee, da ya shahara wajen shirya fina-finan Kannywood ya mika sakorsa kamar haka, ” Wannan babban rashi ne ba ga abokiyar aikin mu ba, Hafsat, har ga mu du duka ne. Ina fatan Allah ya yi wa baba gafara ya sa Aljanna ta zamo makomar sa.

Hafsat ce ta fito jaruma a fim din ‘Gimbiya Sailuba’ wadda Uzee ya shirya. Duk da cewa wannan fim din bai fito ba tukunnan, PREMIUM TIMES, ta ziyarci wuraren da aka shirya wannan fim a Abuja kuma ta ga irin nuna gogewa da bajinta da jaruma Hafsat ta yi a wajen shirya fim din.

Sannan kuma Hafsat ta nuna bajinta da kwarewa a fim din ‘Barauniya’ wanda kusan shine fim din da ya haska ta a farfajiyar fina-finan Hausa.

Share.

game da Author