ZABEN KOGI: Surikai biyu sun ja daga a jihar Kogi a dalilin ko waye sahihin dan takara a PDP

0

Kamar yadda sakamakon zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamnan jihar Kogi na jam’iyyar PDP ya nuna, Musa Wada ne ya lashe zaben fidda gwanin. Sai dai kuma bayan bayyana sakamakon zaben babban abokin takarar sa kuma surikin sa Abubakar Idris ya maka shi a kotu.

Idris ya kalubalanci sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP inda ya ce wai an murde zaben ne domin Wada yayi nasara.

Ya ce kiri-kiri yana kan gaba a lokacin da ake kirga kuri’un zaben sai kwatsam aka turo wasu yan daba suka afka wa wannan wuri suka tarwatsa takardun.

Idris ya ce sam bai yarda ba kuma zai bi hakkin sa ko ta halin kaka domin gaskiya ta bayyana.

Alkalin Kotun da ke sauraren wannan kara ya bayyana cewa ya rika karantawa a shafunan Facebook cewa wai wasu na narka masa makudan kudi domin ya dadada wa wasu rai a yayin yanke wannan hukunci.

” Na yi rantsuwa cewa ba zan yi magudi ba a hukuncin da zan yanke. Saboda haka kowa ya kwantar da hankalin sa ya jira.

Alkalin kotun ya dage zaman kotun zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba domin ci gaba da sauraren masu kare wanda ake kara bayan an yi zaben gwamnan ranar 16 ga wata.

Za a gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi ne a ranar 16 ga watan Nuwamba. Gwamnan jihar Yahaya Bello na jam’iyyar APC ya lashi takobin kada duk wani da zai fafata da shi a kowace jam’iyya ce.

Share.

game da Author