Akalla mutane 10 ne suka rasu a sanadiyyar fama da zazzabin shawara a jihar Bauchi bayan bayyanar cutar a wasu kauyukan dake karamar hukumar Ningi dake jihar.
Wadannan kauyuka kuwa sun hada da Tipchi, Deru, Sabon Gari, Tudun Wada da Barawo duk a gundumar Burra.
Daya daga cikin ma’aikatan asibitin da ya kamu da cutar kuma baya so a fadi sunnansa ya bayyana cewa tun a makonni hudu da suka wuce ne cutar ta bayyana a wadannan kauyuka.
Jaridar ‘Daily Trust’ da ta wallafa wannan rahoto ta rubuta cewa wannan malamin asibiti ya ce tun a farko dai wasu mutane har ashirin ne aka kwantar a asibiti basu da lafiya. Daga baya sai aka rika kawo wasu da dama asibitin har yakai ga dole sai mun aika da su wasu asibitocin dake zagaye da mu.
Bayan haka mai unguwar Tipchi Ilya Mohammed ya yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su gaggauta kawo musu dauki ganin cewa cutar na ta kara yaduwa.
Idan ba a manta ba hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Bauchi (BSHCDA) ta bayyana cewa akalla mutane 23 ne suka rasu a dalilin kamuwa da zazzabin shawara a karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi.
Hukumar NCDC ta ce cutar ta bayyana ne tun daga 29 ga watan Agusta sannan daga ranar 11 ga watan Satumba ta yi wa mutane 169 gwajin jini. Mutane biyar ne aka samu cikin wadanda aka yi wa gwajin na dauke da cutar.
Har yanzu dai hukumar na ci gaba da gwajin jinin mutanen jihar a hedikwatanta dake Abuja.