Babban Hadimin Shugaban Kasa a Harkokin Majalisar Dattawa, Babajide Omoworare, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai maida Mataimakin sa Yemi Osinbajo saniyar-ware ba, don ya yi tafiya bai mika masa mulki ba.
Omoworare ya yi wannan ikirari ne a lokacin da ya kira taron manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Wannan bayani na sa kuwa ya zo ne kwana daya raka bayan Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole ya ce Buhari na iya tafiyar da mulkin kasar nan ko daga wace kasa mai nisa a fadin duniyar nan.
Buhari wanda yayi tafiyar makonni uku, a yanzu haka ya na Landan, kuma ya yi tafiyar ba tare da ya damka mulki ga hannun Osinbajo ba Maimakon haka, sai ya rika gudanar da ayyukan mulki daga can Landan din.
Kwanaki hudu bayan Buhari ya isa London, Shugaban Ma’aikatan Fadar sa, Abba Kyari, ya yi tafiyayya har London, inda ya kai masa dokar jarjejeniyar raba ribas mai tsakanin Najeriya da kamfanoni, ya sa ma ta hannu.
Wannan abu da Kyari ya aikaya, ya janyo ‘yan Najeriya da dama sun rika caccakar salon mulkin Buhari, su na cewa an maida mataimakin sa saniyar-ware.
Wasu da dama na ganin cewa babu wani dalilin da zai sa Kyari ya yi azarbabin yin tattaki har London domin ya kai wa Buhari kudirin doka ya sama masa hannu, tunda makonni biyu kadai zai yi ya dawo.
Gunagunin da wasu ke yi shi ne, don me za a kafci kudaden gwamnati a kashe wajen kai Kyari London don kawai ya kai wa Buhari takarda ya sa ma ta hannu?
Akwai masu cewa rashin adalci ne, domin Buhari ya ma hana Ministoci da manyan ma’aikatan gwamnati fita kasashen waje, sai fa idan akwai wani muhimmin dalili.
Buhari ya yi haka don a rage kashe kudade, amma kuma shi sai kara bijiro da kashe kudade ake ta yi a karkashin ofishin sa.
Wasu kuma gani suke yi an yi haka don kawai a tozarta Osinbajo, a nuna a yanzu an maida shi saniyar-ware.
Sai dai kuma yayin da ya ke wa manema labarai jawabi tare da Babban Mashawarcin Buhari a kan Harkokin Majalisar Tarayya, Umar El-Yakub, Omoworare cewa ya yi Buhari bai yi wa ofishin Mataimakin sa zagon-kasa ba.
Ya kara jaddada cewa Shugaban Kasa na da ‘yancin gudanar da mulkin sa ko daga wace kasa a cikin duniyar nan.
“Ina ganin inda kawai mutane za su iya yin korafi sai idan shugaban kasa ba shi da lafiya, kuma ya kasa aika wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya halin da ya ke ciki, ya yi shiru.
KARANTA NAN: Yadda Abba Kyari ya ‘ribbaci’ Buhari ya kwace Shirin Ruga daga hannun Osinbajo
Idan babu kira me ya ci gawayi?
Yayin da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya na bukatar kudaden da zai fara gagarimin aikin magance rikicin makiyaya da manoma a farkon wannan shekarar, ba shi da masaniyar cewa wani gazagurun mai-fada-a-ji zai shantale masa kafafu har a karshe a kwace shirin daga hannun sa.
To abin da dai ya faru kenan yayin da Osinbajo ya aika da takardar neman amincewa a ba shi kudaden aiki, sai ta kasance Abba Kyari, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ya yi masa zagon-kasa.
Bayan da Kyari ya yi nasarar da ya zuga Buhari ya fasa bai wa Osinbajo kudaden fara aikin gina Ruga, sai kuma ya sa Buhari ya cire shi daga Shugaban Kwamitin Sasanta Rikicin Fulani da Makiyaya, wanda aka dora wa ayyukan gina rugage.
PREMIUM TIMES ta samu wannan tabbacin daga wasu takardun bayanai da za ta iya kafa hujja da su, da kuma hirarrakin da ta yi da wasu mutanen da ke da kusanci da kuma masaniyar kwatagwangwama, kutunguila da annamimancin da ke wakana a Fadar Shugaban Kasa.
Wadannan takardun bayanai na Musamman da yanzu haka kwafen su ke a hannun PREMIUM TIMES, karara sun a nuna irin wulakanci da tozartawar da Osinbajo ke fuskanta, a daidai lokacin da a fadin kasar nan ake ta watsa ji-ta-ji-tar cewa makusantar shugaban kasa su na yi wa Mataimakin sa Osinbajo kallon-hadarin-kaji.