Wani ejan na jam’iyyar PDP a lokacin zaben shugaban kasa na 2019, ya bayyana wa Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa cewa INEC ta yi aringizon rumfunan zabe sama da 1000 a Jihar Barno.
Ya ce INEC ta hada baki da jam’iyyar APC mai mulki ne ta yi wannan aringizon a lokacin da ake gudanar da zaben 2019 cikin watan Fabrairu.
Ejan din mai bayar da wannan shaida, mai suna Nicolas Shediza, shi ne ejan din PDP da ke kula da tattara sakamakon zabe na Jihar Barno.
Ya shaida wa kotu jiya Alhamis a Abuja cewa Jihar Barno na da rumfunan zabe 3,933, amma a lokaci daya sai aka kara su, suka zama 5,078 lokacin zabe.
Shediza ya kara da cewa kuri’u 919, 786, da aka bayyana cewa su aka jefa a Jihar Barno, sun wuce yawan jama’ar da INEC da kan ta ta ce su ne aka tantance katin shaidar rajistar su a lokacin zabe.
Sai dai kuma mai bayar da shaidar bai kawo adadin da ya ce INEC ta ce su ne ta tantance ba.
A cikin wani rahoto dai jaridar Thisday ta watan Fabrairu, ta ruwaito Kwamishinan INEC na Jihar Barno, Mohammed Magaji ya na cewa akwai rumfunan zabe 3,933 a Jihar Barno a fadin kananan hukumomin jihar 27.
Ta ce an yi wa mutane sama da milyan 2.3 rajista.
Shi ma wani mai bayar da shaida, mai suna Jafaru Ibrahim, ya shaida wa kotu cewa fam mai lamba EC8C cike ya ke da ‘‘birkitattun sakamakon zaben da aka jagwalgwala’’ tun daga mazabu da kuma kananan hukumomi.
Ibrahim wanda lauya ne, ya ce ya sanya wa fam EC8C hannu ne domin ya tabbatar da cewa ya na nan kuma ya na da shaidar cewa an jagwalgwala adadin lisaafin kuri’u tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi a cikin fam din mai lamba EC8C.
“Na sa hannu ne ba don cewa na amince da sakamakon ba, sai don na zama shaidar ganin magudin da aka tabka, kamar yadda dokar zabe ta kasa ta jaddada.” Inji Ibrahim.
Shi ma John Makama, wani ejan na PDP daga Jihar Kaduna, ya shaida wa kotu cewa a gaban idon sa aka baddala sakamakon zaben Karamar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna. Ya ce an baddala sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zabe ta karamar hukuma.
Ya zuwa yanzu dai masu gabatar da shaidu guda shida sun gabatar. Jiya ne kuma aka cika rana ta biyar tun bayan fara sauraren karar gadan-gadan, wadda PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar suka kai INEC, Buhari da kuma APC.
Atiku da dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin PDP, Peter Obi sun je kotun jiya Alhamis, domin gabatar da masu shaidu.
Shi ma shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya je a madadin Shugaba Muhammadu Buhari.
Jam’iyyar PDP da PDM da kuma HDP ne ke kalubalantar nasarar da INEC ta ce Buhari ne ya yi a zaben 2019.