SATAR JARABAWA: Kwalejin Fasaha ta kone wayoyin dalibai sama da 1,000

0

Babbar Kwalejin Fasaha ta Badun, wato Ibadan Polytechnic, ta kone wayoyin dalibai sama da guda 1,000, wadanda ta kwace a lokacin da dalibai ke rubuta jarabawa a cikin kwalejin a lokuta da dama.

Wakilinmu ya gano cewa an kwace wayoyin ne daga hannun dalibai daban-daban a lokutan da ake gudanar da jarabawa a makarantar cikin shekarar da ta gabata.

PREMIUM TIMES ta kuma gano cewa an kwace wayoyin ne daga baya kuma aka kone su, domin a rage matsalar satar jarabawa ta hanyar kafofin sadarwa na zamani a kwalejin.

Wayoyin da aka kwace kuma aka kone, sun kama tun daga masu farashin naira 10,000 abin da yayi sama.

An kone Nokia, Tecno, Samsung, BlackBerry da sauran wayoyi samfuran na zamani.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kwalejin Fasahar ne, Bayo Oyeleke da wani babban malamin makarantar suka wakilci makarantar domin sa-ido wurin tabbatar da an kone wayoyin.

Akwai kuma Mataimakin Rajistara, A. O Ayoade, Jami’in Yada Labarai Soladoye Adewale, Babban Jami’in Tsaro Ige Akinsola da kuma Shugaban Kungiyar Daliban Kwalejin Fasaha ta Badun, Akadiri Bayonle.

Oyeleke ya shaida cewa hukumar makaranta ta hana dalibai shiga wa wayoyi a dakin jarabawa, amma kuma sun ki dainawa.

Ya ce saboda sun ki bin doka ne humumar makaranta ta yankec shawarar rika kwace wayoyin ta na konewa.

Kakakin Yada Labarai na Kwalejin, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kone wayoyin ne domin kada a samu kuskure su fada hannayen batagarin mutane.

Ya kara da cewa a kowane lokaci ana gargadin dalibai kada wanda ya sake ya shiga dakin rubuta jarabawa da wayarv hannu. amma kuma basu jin wannan gargadi. Da ake yi musu.

Share.

game da Author