Hukumomin ’Yan Sanda, Majalisa da Masu Shari’a sun fi cin rashawa a Najeriya -Bincike

0

Wata Kungiya mai suna ‘Transparency International’, ta jera hukumomin ’yan sanda, majalisa da fannin shari’a a sahun farko na jerin hukumomin da aka fi cin hanci da rashawa a Najeriya.

Ta buga wannan bayani a jiya Alhamis a cikin rahoton binciken ta na 10.

‘Transparency International’ ta ce munin cin hanci da rashawa a ne ya hana kasashen Afrika yin wani hobbasan inganta tattalin arzikin su, inganta siyasa da kuma ci gaban rayuwan al’ummar su.

“Wannan babbar matsala ta haifar da shingen da ya hana inganta tattalin arziki, ya hana samar da gwamnatoci na nagari sannan kuma ya dakile samun ‘yancin fadar magana domin rika yayata badakalar da shugabanni ke aikatawa.

“Babbar illar kuma ita ce yadda satar kudade ta dakile inganta rayuwar al’umma da samar da ci gaban garuuwan su.

Rahoton ya ce wadannan matsaloli sun yi muni, amma munin wasu yankuna ya fi na wasu sauran kasashen a nan cikin Afrika. Sai dai kuma rahoton ya ce illar da rashawa da wawurar kudade ta yi a Afrika du kusan abu iri daya su ke haifar wa a kowace kasa.

Rahoton Binciken Gejin Rashawa a Afrika dai shi ne rahoton bincike mafi girma da inganci, wanda kungiyar ta ce ta yi bincike kan mutane 47,000 a cikin kasashen Afrika 35.

‘LALATACCE, LALATACCE NE, KO A GIDAN WA’

Kusan kashi 69 bisa 100 na wadanda suka shiga bada amsoshi a binciken sun zabi cewa ‘yan sanda sun fi kowane fanni lalacewa wajen cin hanci da rashawa. Daga su kuma sai mambobin majalisa da kashi 60 bisa 100 suka ce su ne suka fi lalacewa bayan hukumar ‘yan sanda.

Masu Shari’a ne jama’a kashi 51 bisa 100 suka ce su ne na uku wajen lalacewa. Daga su kuma sai manyan ma’aikatan gwamnati, wadanda kashi 40 bisa na mutanen da aka yi wa tambayoyi suka ce su ne na hudu wajen lalacewa.

Sauran kashi 55 bisa 100 suka zabi ma’aikatan kananan hukumomi, wasu kashi 54 hudu kuma suka ce jami’an gwamnati, yayin da kashi 40 bisa 100 suka ce kungiyoyin sa kai ne lalatattu wajen rashawa da cin hanci.

Akwai wadanda suka ce manyan ‘yan kasuwa ne, wasu kuma suka ce masu rike da sarautun gargajiya, yayin da kuma kashi 20 bisa 100 suka ce shugagabbnin bangarorin addinai a sahun karbar cin hanci da rashawa.

Sannan da dama kamar kashi 42 bisa 100 sun zabi cewa cin hanci da rashawa karuwa ma ya yi, ba raguwa ya yi a cikin watanni 12 da suka gabata.

Share.

game da Author