Tun da sanyin safiyar Talata ne masu garkuwa suka sako Magajin Garin Daura Musa Umar, dake tsare a wajen su wata biyu kenan.
Daya daga cikin ‘ya’yan mafajin gari, Bashar ne ya tabbatar wa PREMIUM TIMES sakun mahaifinsu da masu garkuwa suka yi.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne mutanen garin Daura suka yi addu’o’i domin Allah ya kubutar da Magajin Gari Umaru.
‘Yan sanda sun ce an sako Magajin Gari Umaru a Titin zuwa Madobi, dake jihar Kano ranar Talata.