ZABEN 2019: Jam’iyya daya ce ta gabatar wa INEC yadda ta kashe kudin kamfen –Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa har zuwa yau din nan, jam’iyya daya tal e ta mika wa INEC bayanan yadda ta kashe kudade a wurin kamfen din zaben 2019.

Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce duk da doka ta jaddada cewa tilas kowace jam’iyya ta bayyana wa INEC yadda ta samu kudaden ta da kuma yadda ta kashe su dalla-dalla, amma har yau jam’iyya daya kadai ce ta bi wannan umarni, watanni uku bayan kallama zabukan.

Yakubu ya yi wannan korafin jiya Litinin Abuja, yayin da ya ke jawabi a wurin taron nazari da bitar yadda aka gudanar da zabukan 2019.

INEC ta shirya taron ne tare da jam’iyyun siyasa wadanda suka shiga zaben 2019.

Farfesa Yakubu ya ce har zuwa yau din nan, dan takarar shugabancin kasa daya ne ya damka wa INEC bayanan yadda ya kashe kudade da kuma iringudummawar da ya samu a wajen yakin neman zaben shugaban kasa na 2019.

Ya ce wannan kuwa doka mai karfin gaske a cikin Dokokin Zabe, amma abin takaici, babu wata jam’iyya da ta cika wadannan sharudda na doka, wadda ta tilasta wa jam’iyyu su sanar wa INEC yadda suka samu kudaden gudummawa daga daidaikun jama’a ko kuma kungiyoyi ko wasu kamfanoni domin tallafa musu wajen kamfen.

“Ina kara tunatar da ku cewa Dokar Zabe ta 2010 da aka yi wa kwaskwarima, ta bukaci dukkan jam’iyyu da su mika wa INEC kwafe biyu na bayanan kudaden da suka kashe a lokacin kamfen.

” Na farko shi ne a bayyana wa INEC dalla-dallar adadin kudaden gudummawa da kuma sunayen wadanda suka bayar da gudummawar akalla watanni uku bayan kammala zabe. Sashe na 93(4) na Dokar Zabe ne ya tilasta haka.

“Amma dai ya zuwa yanzu babu jam’iyya ko daya ba ta bi wannan umarnin, ko kuma a ce ta cika wannan umarni.

“Bayanai na biyu kuma su ne kowace jam’iyya ta gabatar wa INEC dalla-dallar yadda ta kashe kudade a wajen kamfen, akalla watanni shida bayan kammala zabe, kamar yadda Sashe na 92(3) (a) na Dokar Zabe ya tilasta.

“Duk da dai har yanzu mu na cikin lokacin da za a iya kawo wadannan rahotanni, har yanzu jam’iyya daya ce tal ta gabatar wa INEC yadda ta kashe kudaden na ta.

A kan haka ne Farfesa Yakubu ya sake tunatar wa jam’iyyun siyasa irin nauyin da ke kan su wanda ya ce dokar kasa ce ta gindaya, kuma tilas su bi doka.

Daga nan ya kara da cewa sai sun gina kyakkyawar hanyar inganta jam’iyyu sannan za a samu dimokradiyya mai inganci a kasar nan.

Daga nan kuma ya nuna musu cewa akwai matasala sosai dangane da yadda yawancin jam’iyyu suka gudanar da zaben fidda-gwani. Wadannan matsaloli a cewar sa, sun haifar da tulin shari’un da ake fama da su a kotunan kasar nan daban-daban.

“A zaman yanzu haka akwai kararraki har guda 809 na zabukan fidda-gwanin jam’iyyu da ke a gaban kotuna daban daban. Wadannan kuwa sun ma fi yawan kararrakin korafe-korafen zabukan 2019 da ke a gaban kotuna daban-daban.”

ZABEN GWAMNA A KOGI DA BAYELSA

Dangane da zaben gwamna da za gudanar a jihohin Kogi da Bayelsa kuwa, a ranar 16 Ga Nuwamba, Yakubu ya ce ya zuwa yanzu dai jam’iyyu uku ne suka sanar wa INEC ranakun da za su gudanar da zaben fidda-gwanin ‘yan takarar su.

Yakubu ya kara nanata cewa ranar 5 Ga Satumba ce za INEC za ta rufe yin zabukan fidda-gwani a Bayelsa da Kogi.

Don haka duk jam’iyyar da ta gudanar da zaben fidda-gwani bayan 5 Ga Satumba, to INEC ba za ta amince da sakamakon zaben ba.

A karshe ya shawarci jam’iyyun da za su shiga zaben da cewa su tabbatar sun yi zaben fidda-gwani mai tsafta kuma mai adalci ba tare da rigingimun da za a afka neman mafita a kotuna bayan kammala zabukan ba.

Share.

game da Author