El-Rufai ya ziyarci Cocin St. Augustine da aka cinna wa wuta a Kaduna

0

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ziyarci Cocin St. Augustine da aka cinna wa wata a daren Juma’ a a Kaduna

Duk da cewa ba haryanzu ba a tabbatar da ko su wanene suka cinna wa wannan Coci wuta ba tun a washe garin ranar ne wani jami’an gwamnati ya ziyarci wannan Coci domin jajanta wa cocin.

Wasu da ba a san ko su waye ba sun cinna wa cocin dake Tududn Wadan Kaduna wuta inda ya kone wasu sassan cocin.

Hakan bai hana mabiya gudanar da ibadar bauta ba ranar Lahadin da ya gabata.

A ranar Litinin, gwamna El-Rufai ya ziyarci Cocin da kansa inda ya kai ziyara gani wa kansa abin da ya faru sannan ya yaba wa daliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Kaduna bisa namijin kokarin da suka yi wajen fitowa cikin daren domin kashe wutar da aka cinna wa Cocin.

Samuel Aruwa, daya fitar da matsayar gwamnati akan wannan hari da aka kai wa Cocin ya ce tuni har an kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a aikata wannan ta’asa.

Sannan kuma gwamnatin jihar ta yabawa wa shugabannin Cocin da mabiyan su bisa gudanar da ibada da suka yi a safiyar ranar.

Share.

game da Author