HARKALLAR BANKIN HABIB: Idan Atiku ya dawo zai sha Tambayoyin gaske – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya bayyana wa manema Labarai cewa da zarar dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dawo kasar nan daga balagoron sa a kasar Amurka zai fuskanci matsananci tambayoyi daga hukumomin Najeriya.

Lai Mohammed ya kara da cewa, zuwan sa kasar Amurka bai dada gwamnatin Najeriya da kasa ba sai dai ya tunasar da mutane cewa lallai gwamnati basu so haka ba domin har shawara suka aika wa kasar Amurka din da kada su barshi ya koma shiga kasar.

” Wai don ya tafi kasar Amurka, wannan hukuncin kasar ne amma Atiku ya sani cewa da zarar ya dawo kasar nan zai fuskanci hukumomin domin amsda tambayoyi game da wasu kudade har naira miliyan 150 daga tsohuwar Bankin Habib.

Ya ce a ranar 13 ga watan Janirun 2009, Atiku ya karbi naira Miliyan 150 a wannan banki da duk yana daga cikin dalilin da yasa wannan banki ta ruguje.

“Idan ya ga dama ya ci gaba da zama a kasar Amurka, kai suma bashi katin zam na dindindin, amma fa ya sani cewa da zarar ya dawo kasa Najeriya gwamnati na nan tana jiran shi ya zo yayi bayanin wannan kudi sannan ya fadi inda suke. Kuma ya sani cewa zabe fa ba a Amurka za ayi ba, a Najeriya za ayi kuma ya sani zai sha kasa.

Share.

game da Author