Wasu masana kimiyyar itatuwa sun bayyana cewa itacen bagaruwa, ganyenta da ‘ya’yan ta na maganin cututtuka a jikin mutum masu yawa.
Ana yin noman itacen Bagaruwa a kasashen da suke da rana da hamada. Kasashe kamar su Australia da yankin kasashen Larabawa na daga cikin kasashen da aka fi noma itacen.
Ba mutum dan adam ba masanan sunce itacen bagaruwa na yi wa dabbobi ma maganin cututtuka a jikin su.
Ga amfanin da yake yi a jikin mutum./strong>
1. Bagaruwa na maganin tsutsan ciki.
2. Yana maganin gudawa.
3. Yana kuma kawar da matsalar zuban jini.
4. Bagaruwa na maganin ciwon hakori.
5. Yana kuma maganin ciwon siga wato ‘Diabetes’.
6. Bagaruwa na kawar da warin jiki da warin baki.
7. Yana magani da hana kamuwa da cutar sanyi.
8. Yana maganin matsalar ciwon ido kamar su jan ido da kwantsar ido.
9. Yana kara karfin mazakuta.
10. Bagaruwa na maganin cutar Hepatitis C
Discussion about this post