Dalibai 300,000 sun yi rajistar jarabawar JAMB a cikin mako daya

0

Jami’in hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’in Kasa, JAMB, Fabian Benjamin ya bayyana cewa hukumar ta yi wa dalibai 300,000 rajista a cikin mako daya da fara siyar da fom din jarabawar.

Benjamin ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jihar Legas ranar Juma’a.

Ya ce hukumar ta gamsu matuka tun da ta fara siyar da fom din jarabawar ranar 10 ga watan Janairu 2019 sannan tana sa ran rufe siyar da fom din ranar 21 ga watan Faburairu.

” Daga cikin dubban daliban dake kokarin siyan fom din, 300,000 sun yi rajista sannan tun da muka fara siyar da fom din ba mu sami matsala ba tukuna.

A karshe kungiyar iyaye NAPTAN ta yi kira ga JAMB da ta bude sashen da za a rika gyara matsalolin da dalibai kan yi fama da su wajen yin rajista sannan kuma ya ce wadanda suka sami matsala a jarabawar ko rajista za samu daman yin jarabawar ne a hedikwatar hukumar jarabawar da ke Abuja.

Share.

game da Author