Ghali Na’abba ya fice daga APC

0

Tsohon kakakin majalisar wakilai Ghali Na’abba ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC.

A doguwar wasika da ya rubuta, Ghali ya bayyana cewa barankadamar da ya cukuikuyi jam’iyyar APC na daga cikin abubuwan da ya sa yaga ba zai iya ci gaba da zama a irin wannan jam’iyya ba.

” Ku duba ko abin da ya faru a majalisar kasa, irin haka na da nasaba ne da lalacewa da rashin iya mulki da gwamnatin APC ta kagara yi a kasa Najeriya.

” A rashin iya shugabanci da rike duk ‘yan jam’iyya a matsayin tsintsiya madaurinki daya ya sa a gaban su suka rasa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

” Duk ta inda kabi zaka ga an toshe sannan idan har kana so ayi yadda yaka mata ne ko kaba da shawara sai dai ka koma ka zama dan amshi shata.

” Na yi kokarin a gyara amma abin ya kagara.

Duk da cewa Ghali bai fadi inda ya dosa ba ko kuma jam’iyyar da zai koma, alamu sun nuna zai koma jam’iyyar PDP ne.

Share.

game da Author