An Karrama wadanda suka ci gasar yin na’uran yin gwajin cutar Kanjamau

0

Kungiyar 4Youth By Youth (4YBY) ta karama wasu matasa uku da suka ci gasar yin na’uran gwajin cutar kanjamau da mutum zai iya amfani da shi da kansa ba sai ya tafi asibiti ba.

4YBY ta karrama wadannan matasa ne a taron wayar da kan mutane game da cutar kanjamau da aka yi ranar Legas.

Matasan da suka ci wannan gasa sun hada da Tony Akeju, Ginika Nzokwe da Idris Badmus.

Ita wannan na’ura za a iya yin gwajin ko da jini ko kuma yawun baki.

Gasar ya samar wa wadannan matasa kyaututtuka da dama sannan kuma an basu gurbin karo karatu a makarantar bincike dake North Carolina a kasar Amurka.

Jami’ar kungiyar 4Youth By Youth Juliet Iwelunmor ta bayyana cewa ” Najeriya ce ta uku cikin jerin kasashen Afrika da suka fi yawan mutanen dake fama da cutar kanjamau. Sannan kuma babbar illar shine da yawa daga cikin masu dauke da cutar ba su san suna dauke da cutar ba.

A karshe ta yi kira ga mutane da su je ayi musu gwajin cutar domin hakan shine zaman lafiyar su.

Share.

game da Author