Ba a banza jama’a da dama ke korafi da kiraye-kirayen a yi wa rundunar ‘yan sandan kai daukin gaggawar dakile fashi da makami, wato SARS, kwaskwarima ba. Wasu ma cewa su ke yi a ruguza rundunar kawai.
Bari mu dauki labarin abin da ya faru da Oluwaseyi Adesuyi, wanda jami’an SARS suka kama. Rabon da a ji labarin inda ya ke ko halin da ya ke ciki, tun a ranar 15 Ga Yuli, 2013, lokacin da SARS suka gabatar da shi a gaban ‘yan jarida, bisa zargin sa da ake yi da laifin garkuwa da mutane.
Tun daga ranar, har yau din nan, mutumin ya bace, babu labarin sa, an rasa inda ya ke.
SARKAKIYA
’Yan sanda, wadanda dama su ne suka kama shi, kuma suka gabatar da shi a gaban ‘yan jarida, sun kasa bayyana abin da ya faru da shi. Sun kasa gabatar da duk wani rubutaccen bayanin kama shi, ko yadda aka yi suka kama shi, ko ma inda suka kama shi. Bai dai tsere daga hannun ‘yan sanda ba, kuma babu wata hujja rarrauna ko kwakkwara da ke nuna cewa an gabatar da shi kotu, ballantana a ce ya na kurkuku a tsare.
NEMAN ADESUYI RUWA A JALLO
Iyalan Adesuyi sun yi ta neman maigidan na su a kowane ofishin ‘yan sanda a jihohin Lagos, Ondo, har da Abuja, amma ba su cin karo da komai, sai dai bayanin cewa ba a san abin da ya faru da shi ba.
LAIFIN DA AKE ZARGIN YA AIKIATA
Oluwaseyi, wanda bai kammala Babbar Kwalejin Ilmi ta Adeniran Ogunsanya, da ke jihar Ondo ba, sai ya daina karatun, ya na cinikin wayoyin hannu ne da kuma kananan kwamfutocin tafi-da-gidan-ka na laptops, a kasuwar Alaba da ke Lagos.
A cikin watan Yuni, ya na tuki a cikin unguwar Okokomaiko, Lagos, sai wasu da suka ce jami’an SARS ne, suka tare shi, kuma nan take suka kwace masa motar sa, samfurin Nissan Pathfinder SUV.
‘Yan sandan sun caje shi da cewa ya sayi kwamfuta laptop wacce aka sata daga wani mai suna Kehinde Bamigbetan, wanda a lokacin da aka ce an yi satar, ya na shugabancin karamar hukumar Ejigbo. Amma a yanzu Kehinde Kwamishina ne na Yada Labarai, a karkashin gwamnatin jihar Lagos.
Kehinde ya tsira daga wadanda suka sace shi, bayan ya yi kwanaki bakwai a hannun su tare da biyan diyyar kudade
INA OLUWASEYI YA KE NE?
Bayan kwanaki uku ba a ji labara ko duriyar Adesuyi ba, kuma wayar sa a kashe, sai abokan sa suka kira iyayen sa da ke zaune a Akure, domin su tambaya su ji ko su na da labarin dan su Adesuyi.
Iyayen sa sun damu matuka, kuma hankulan su ya tashi, inda mahaifin sa ya tashi ya bazama neman inda dan sa Oluwaseyi Adesuyi ya ke.
Ya yi ta neman sa a ofisoshin ‘yan sanda da ma wasu wurare da dama, har bayan kwanaki da yawa, amma babu labarin inda ya ke.
Mahaifiyar sa Elizabeth hankalin ta fa ya tashi, har ta rika sambatu ta na cewa: “Da irin wannan tashin hankali da na shiga a ciki, har gara ma a ce dan mutum mutuwa kawai ya yi.”
Ba ta dai hakura ba, ta yi ta addu’o’i har da azumi. A nan nan rannan sai addu’ar ta ta samu karbuwa.
Yadda aka yi kuwa, wani ne ya ba su shawarar cewa kamata ya yi a je ofishin SARS da ke Ikeja a bincika a gani ko za a dace idan ya na can.
AL’AJABI A OFISHIN SARS: Ga sunan wanda ake nema, amma babu shi
Suka kuwa je ofishin SARS, suka bincika. Aka dauko rajistar wadanda ake kamowa aka tsarewa, aka yi sa’a sai ga sunan sa a cikin littafin rajista.
Sai dai kuma maimakon a gabatar musu da dan su su yi ido da ido da shi, duk sai jami’an SARS suka yi turus, aka yi carko-carko!
“Mu ka tambaye su ina dan mu? Babu amsa! Me ya faru da shi? Babu amsa! Me ake ciki ne? Kowanen su ya yi shiru! Duk da haka ba mu hakura ba, mu ka rika zuwa ofishin a kullum. Mu dai ba mu gan shi ba. Amma tunda sun ce ya na hannun su doming a sunan sa mun gani a rajista, sai muka kaddara cewa ya nan da ran sa.” Inji Elizabeth.
Sun ce jami’in da batun dan su ke hannun sa, ana kiran sa ne da lakabin Jamaica. Ba su san sunan sa ba, domin babu mai kiran sa da sunan sa na ainihi, sai Jamaica. Kuma ba su sanya kakin ‘yan sanda ballantana a gane mukamin sa.
Sai dai kayan gida suke sa wa ko kuma bakar rigar nan ta aiki, mai dauke da sunan SARS.
“A karshe, sai suka ce mana wanda mu ke nema din nan, dan fashi da makami ne, don haka ba za mu iya ganin sa ba. Har yau kuma ba mu sake ganin sa a idon mu ba tun daga ranar da aka kama shi.” Inji Elizabeth.
YADDA WANI DAN SANDA YA DAMFARI IYAYEN OLUWASEYI
Makonni da dama bayan iyayen sa sun yi ta zuwa ofishin SARS ba tare da samun nasarar ganin dan su ba, sai wani mutum ya kira su a waya, ya ce masu a cikin kurkukun ‘yan sanda daya aka kulle shi da Oluwaseyi, amma ba laifi iri daya ake tuhumar su da shi ba.
Mutumin ya ce dama Oluwaseyi ne ya ba shi lambar iyayen na sa, ya ce idan ya fita daga hannun hannun ‘yan sanda, to ya kira su domin ya shaida musu halin da dan na su ke ciki.
Mutumin ya shaida wa Elizabeth, mahaifiyar Oluwaseyi cewa akwai wani jami’ain dan sandan da za su yi wa magana domin ya taimaka a sake shi.
“Mu ka kira lambar da ya ba mu, sai aka ce mana ai wayar da dan mu suka saida daga hannun dan fashi ya saye ta, kuma motar da dan na mu ya ke hawa, wai ita ma a hannun dan fashi ya saye ta.’’
Daga nan ta ci gaba da cewa wannan dan sanda bai bayyana kan sa ba, sai ma ya nemi a ba shi naira 200,000.00, domin ya taimaka a saki Oluwaseyi.
Ya ce sun nemi kudin sun ba shi, saboda su na so su ga dan su, su kuma ga halin da ya ke ciki. Sai dai kuma bayan da suka biya kudin, sai wannan dan sanda ya yi ta neman karin kudi a hannun su.
Yayin da suka ce masa ba su da hanyar samun wasu kudin da za su ci gaba da ba shi, sai ma ya daina daukar wayar su, ya rika yi musu walle-walle. Daga nan sai suka fahimci ya daina amfani da lambar wayar da suke kiran sa. Karshe ma sai suka gano cewa ya yi ritaya daga aikin dan sanda.
A SANAR DA NI HALIN DA DA NA KE CIKI -Elizabeth
Elizabeth ta na magana murya ta na rawa, ta yi rokon a taimaka a sanar da ita halin da dan ta ke ciki. Ta ce dan ta ba mai fitina ba ne, kuma shi ba barawo ba ne. Wayoyi ya ke sayarwa wadanda ake shigo musu da su ne daga China.
BA MU TASKACE SUNAYEN WADANDA MU KE KAMOWA – SARS
Yayin da wakilin mu ya ziyarci ofishin SARS da ke Ikeja, inda a can ne aka yi wa Oluwaseyi ganin karshe, an shaida masa cewa babu yadda za a yin ya iya sanin yadda ta karke da shi.
Shugaban SARS na Ikeja, Peter Gana, wanda Babban Sufurtanda ne, ya ce bai dade da kama aiki a wurin ba. Daga watan Yuli ya fara, kuma shi ne babban jami’i na biyar da aka yi a wurin tun 2013, bayan kama Oluwaseyi da ake magana.
“Ba zan iya taimakon ka dangane da abin da ka ke neman sanin ba, saboda ba ka da sunayen jami’an da ke aiki a lokacin da abin ya faru.” Inji Gana.
WALLE-WALLE A OFISHIN SARS
Da aka tambaye shi me zai hana ya bincika a cikin littafin da suke taskace bayanai da ranaku da shekaru, tunda sunan wanda ake zargin ya bace din na nan, sai Gana ya ce su wannan ofishi na su ba ya adana rekod na bayanan kamammun da ake tsarewa a caji ofis na su na SARS.
“Idan ma na dauke ka na kai ka inda ake adana bayanan, za ka ga ba kimtse suke ba. Komai a hargitse, wani a kan wani, kuma tarwatse a kan dabe. Wasu ma sun jike da laimar ruwa. Kai ko da ma mun ga takardun bayanan, to ina tabbatar maka ba za su iya karantuwa ba, domin ruwa ya jike rubutun yadda ba zai karantu ba.” Haka Gana ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES, yayin da ya je binciken kwakwaf a ofishin SARS.
Gana ya ci gaba da cewa shi kan sa ya koyi darasi, domin duk wani batu da ya shafe shi kai tsaye, to ya na yin kwafe guda na bayanan ya adana a gidan sa.
Sai ya ce ya na yin haka ne domin gudun kada bayanan su salwanta a yi ta kame-kame.
Har ma ya buga wa wakilin mu wani misali, ya ce an nemi wasu bayanai na abin da ya faru a cikin watan Fabrairu, 2018, aka rasa. Ya ce shi ya sanya tun daga lokacin ya shiga taitayin sa, ya rika yin kwafe na bayani ya na taskacewa a gida, saboda gudun tashin-tashina wata rana.
A karshe, shugaban SARS Gana na Ikeja, Lagos, ya shawarci wakilinmu da ya tuntubi Abba Kyari, domin shi ne shugaban SARS na wurin a cikin 2013. Shi ne ya fi dacewa yay i bayani dangane da inada Oluwaseyi ya ke.
Yayin da aka tambayi Abba Kyari, wanda a yanzu shi ne shugaban rundunar RRS, da Sufeto Janar Ibrahim Idris ya kafa, sai ya buga rantsuwa ya ce, “wallahi ba zan iya tunawa ba ko wane mutum ne ake magana a kai ba, domin abin ya dade. Amma me ya sa tun tsawon wancan lokacin ba su neme shi ba sai yanzu?