HARIN MATELE: Sojoji 118 ne suka rasu, 153 har yanzu ba a san inda suke ba

0

Zuwa yanzu an tabbatar da rasuwar sojoji 118 sannan wasu 153 sun bace har yanzu ba asan inda suke ba.

Idan ba a manta ba daya daga cikin sojojin da suka tsira daga harin da Boko Haram suka kai wa barikin Metele, karamar hukumar Guzamala jihar Barno ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shima Allah ne yasa zai tsira da ran sa a wannan hari domin kuwa sojojin Najeriya da ke aiki a wannan bariki basu sha da dadi ba.

Ko da yake tun kafin wannan hari, sai da Boko Haram suka aika wa Sojojin sakon cewa zasu kawo farmaki barikin. Ba nan ba kawai har da wasu dake Kauyukan Barno.

” Boko Haram sun far wa barikin mu ne ranar litini da misalin karfe 6 na yamma.

” A lokacin da sojan da ke can kololin sama wato mai hangen nesa daga barikin ya sanar mana cewa ga fa gungun mayakan Boko Haram nan sun kunno kai zuwa wannan bariki sai dukkan mu muka daura damara muka ja daga muna jiran su.

” Gaba daya batakashin bai dauke mu tsawon mintuna 45 ba domin mayakan Boko Haram din sun fi karfin mu a dalilin manyan makamai da suke dauke da su.

” Da muka fahimci cewa ba za mu yi galaba a wannan batakashi da muke yi da ‘yan Boko Hama din ba sai muka nemi mu gudu. Hakan shima yayi mana wuya matuka domin barikin a zagaye yake da yawa sannan kuma ta hanya daya da ake shiga barikin kuma ta nan ne suke bude mana wuta – Yadda Boko Haram suka yi wa barikin Metele diran mikiya suka kashe sojoji 75

A dalilin wannan tashin hankali da ya auka wa sojojin Najeriya dake barikin Matele, ranar Juma’a Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa shi da manyan hafsoshin tsaron kasar nan.

Taron na gaggawa ya biyo bayan mummunan kisan da aka ruwaito mayakan Boko Haram sun yi wa sojojin Najeriya a sansanin su da ke kauyen Metele da ke kan iyaka da kasar Chadi.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito cewa taron zai maida hankali ne wajen abin da ke faruwa a fagagen dagar sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas.

NAN ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta yi jinkirin yin magana ne dangane da yawan sojojin da aka kashe, saboda ana ta kokarin tantance yawan su da kuma tuntubar fara sanar da iyalan su tukunna.

Wasu rahotanni dai sun ce an kashe sama da sojoji 44 a mummunan harin da Boko Haram suka kai wa sansanin sojoji da ke Metele, wani surkukin kauye da ke cikin karamar hukumar Guzamala, jihar Barno.
Guzamala na kan iyakar Barno da Chadi ne.

Hukumar tsaro ta sojojin Najeriya su ma daga bayana sun yi bayani, tare da yin korafin yadda aka rika yayata batun kisan.

“Ya kamata jama’a su sani a tsari da da kuma doka ta aikin soji, ba daidai ba ne a rika yada labarin wadanda suka rasa ruyukan su, har sai bayan an gama tuntubar iyalan su an sahaida musu tukunna.”

Tun da farko Shugaba Buhari ya aika Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali zuwa kasar Chadi domin yin taron gaggawa da shugaba Idris Deby dangane da yadda tsaro ya tabarbare a kan iyakar kasashen biyu.

Tun a ranar Alhamis Dan-Ali ya gabatar wa Buhari rahoton halin da ake ciki a yankin na Tafkin Chadi, har da labarin kashe wasu sojojin Najeriya da ‘yan ta’addar IWAP, wata kungiyar zafin kan ta’addanci da ta balle daga Boko Haram da ke karkashin Shekau, kuma ta ke cin Karen ta babu babbaka a yankin kan iyakar Najeriya da Chadi.

Majiya ta ce Dan-Ali zai zauna da takwaran sa Ministan Tsaro na Chadi domin jin yadda aka kashe dimbin sojojin Najeriya a yankin.

Majiyar da ta nemi a sakaya sunan ta ta bayyana cewa: “Maganar gaskiya Najeriya na fuskantar matsala daga Chadi, a shiryin gamayyar sojojin MNJIFna kasa da kasa da aka kafa a Yankin Tafkin Chadi domin kakkabe ta’addancin da a ke yi a yankin.”

Majiyar ta tabbatar da cewa Chadi na da matsalar ta daban ta cikin gida, shi ya sa ma ta kasar ta cire sojojin ta daga cikin shirin gamayyar sojojin kasa-da-kasa din da ke kan iyaka.
“To wannan matsala ce ta sa a yanzu Boko Haram ke kutsawa kan su tsaye cikin Najeriya, Kamaru da Nijar su na kai hari bagatatan.”

Idan ba a manta jiya PREMIU TIMES HAUSA Ta ruwaito Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama Abubakar Saddique ya furta cewa za a kafa sansanin sojojin sama a Jamhuriyar Nijar, a garin Diffa, wanda zai rika kai wa Boko Haram hari.

Share.

game da Author