RA’AYOYIN KU: Shin BUHARI ya halarci taron mahawara da za ayi da ‘yan takarar shugaban kasa ko A’a?

0

Shin BUHARI ya halarci taron mahawara da za ayi da ‘yan takarar shugaban kasa ko A’a? Wannan shine tambayar da mukayi wa masu kartu a shafin mu na Facebook domin sanin ra’ayin su game da shirin da ake yi yi wa masu takarar shugaban cin Najeriya muhawara domin kowa ya bayyana wa yan Najeriya abin da za su yi musu idan suka dare kujerar mulki.

Masu karatu da dama sun bayyana cewa ba lalli sai shugaba Buhari ya halarci wannan taro ba domin kuwa abubuwan da yayi ya isar masa ba sai ya fadi ba.

Kungiyar nan Mai Hada Maharawa a Kafafen Yada Labarai ta Najariya, ta sa ranar da za a gudanar da mahawara tsakanin masu takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Sanarwar ta ce za a yi mahawa tsakanin masu takarar mataimakin shugaban kasa a ranar 14 Ga Disamba, 2018, yayin da za a tafka mahawara a tsakanin masu takarar shugaban kasa a ranar 19 Ga Janairu, 2019.

Za a gudanar da mahawarar ce a Otel din Hilton, Abuja.

Mahawarar za ta fi karfi ne kacokan a kan tattalin arziki, wutar latarki, samar da aikin yi, harkokin kiwon lafiya, tsaro da sauran su. Haka masu shirya mahawarar suka bayyana.

Sai dai kuma ba a tabbatar ba ko manyan ‘yan takara sun nuna amincewar shiga mahawarar ba.

A wadda aka shirya kafin zaben 2015 dai Buhari bai shiga ba, amma Goodluck Jonathan ya shiga.

Sai dai kuma shugaban wannan kungiya mai suna Jimoh Momoh, ya yi kira da a kafa dokar da za ta tilasta wa kowane dan takara fitowa a tafka mahawara da shi, domin ya bayyana wa masu zabe irin kamun ludayin da za ya yi wa mulkin sa idan har ya yi nasara.

Ga wasu daga cikin ra’ayoyin masu karatu:

Share.

game da Author