Daya daga cikin sojojin da suka tsira daga harin da Boko Haram suka kai wa barikin Metele, karamar hukumar Guzamala jihar Barno ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shima Allah ne yasa zai tsira da ran sa a wannan hari domin kuwa sojojin Najeriya da ke aiki a wannan bariki basu sha da dadi ba.
Ko da yake tun kafin wannan hari, sai da Boko Haram suka aika wa Sojojin sakon cewa zasu kawo farmaki barikin. Ba nan ba kawai har da wasu dake Kauyukan Barno.
” Boko Haram sun far wa barikin mu ne ranar litini da misalin karfe 6 na yamma.
” A lokacin da sojan da ke can kololin sama wato mai hangen nesa daga barikin ya sanar mana cewa ga fa gungun mayakan Boko Haram nan sun kunno kai zuwa wannan bariki sai dukkan mu muka daura damara muka ja daga muna jiran su.
” Gaba daya batakashin bai dauke mu tsawon mintuna 45 ba domin mayakan Boko Haram din sun fi karfin mu a dalilin manyan makamai da suke dauke da su.
” Da muka fahimci cewa ba za mu yi galaba a wannan batakashi da muke yi da ‘yan Boko Hama din ba sai muka nemi mu gudu. Hakan shima yayi mana wuya matuka domin barikin a zagaye yake da yawa sannan kuma ta hanya daya da ake shiga barikin kuma ta nan ne suke bude mana wuta.
” Daya daga cikin matukan motocin yakin mu ya nemi ya bita jikin wannan waya da karfin tsiya. A daidai yana kokarin haka ne motar sa ta kafe a wurin. A nan ne fa Boko Haram suka yi mana kisan kare dangi. Suka rika yi mana barin wuta inda nan take suka kashe kusan duka sojojin dake cikin wadannan motoci da wadanda ke zagaye.
” Wadanda suka samu suka gudu kuwa sun tsinci kan su ne a kauyen Kauwa inda suka yi ta hawa motoci da babura zuwa garin Maiduguri duk kuwa dauke da rauni a jikkunan su.
Wannan soja ya shaida mana cewa bayan wannan kisa da Boko Haram suka yi wa sojojin sun tafi da motocin yaki har bakwai daga wannan bariki.