BOKO HARAM: Sojoji sun saki bidiyon korafin rashin makamai na zamani da cuwa-cuwar da kwamandojin su ke yi

0

Wasu sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram, sun saki faifan bidiyo sun a zargin kwamandojin su ne ke jagorantar su zuwa abin da suka kira ‘mayankar Boko Haram’.

Sun kuma yi kukan rashin makaman da za su yi yaki na zamani a daidai lokacin da su kwamandojin ke azurta kan su da kudaden makaman da ake warewa domin a sayi makamai da su.

Bidiyon dai ya yi dishi-dishi, wanda hakan ke nuni da cewa da kyamarar wayar selula aka yi rikodin din sa. An rika nuno sojojin Najeriya su na bayyana damuwar su a cikin zafafan kalamai.

Wani jami’in soja ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sojoji da yawa da aka kashe a cikin bidiyon an kashe su ne a harin Metele, amma dai ba a tantance ikirarin na sa ba tukunna.

Faifan bidiyon mai dauke a cikin minti 5 da sakan 51, wata majiyar cikin sojoji ta bayyana cewa ann dauke shi ne jim kadan bayan da aka yi wa sojoji mummunan kisa a harinn farko da Boko Haram su ka fara kai wa a sansanin Metele, a ranar 8 Ga Oktoba.

Makonni kadan ne kuma Boko Haram suka sake kai wani mummunan hari a wannan sansani wanda dukkan hare-haren sai da PREEMIUM TIMES Hausa ta kawo su dalla-dalla.

Wannan jarida kuma ta buga labarin bidiyon da Boko Haram suka yadawa, mai nuna irin barnar da suka yi wa sojojin Najeriya a wannan hari da suka kai a sansanin Metele da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Chadi.

Ranar Juma’a sojoji sun tabbatar da harin da Boko Haram suka kai a sansanin Metele, amma ba su fadi adadin wadanda suka rasa rayukan su ba.

Sai dai kuma har yanzu sojoji ba su yi magana a kan bidiyon da Boko Haram suka yi ikirarin fitarwa ba.

Idan ba a manta ba, Hafsan Hafsoshin Soja, Tukur Buratai ya sha jaddada cewa ana bai wa sojoji duk wani abin da ya wajaba a ba su, duk kuwa da yawan korafe-korafen da ake ruwaitowa a kafafen yada labarai sojoji na yi.

Watanni uku da suka gabata kuma, Buratai ya gargadi sojoji cewa su daina juyawa da gudu daga farmakin Boko Haram.

Buratai ya yi musu barazanar cewa duk wanda aka kara samu ya juya da gudu daga yaki da Boko Haram, to za a hukunta shi.

Cikin makon da ya gabata ne kuma Hedikwatar Tsaro ta Sojoji ta yi sanarwar aikawa da muggan makamai ga sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram, har ta cika bakin cewa kwanan nan Boko Haram za su gane kuren su.

TULIN TSOFFIN MOTOCIN YAKI

A cikin wannan bidiyon korafi da wasu sojoji suka fitar, an rika nuno tsoffin motocin yakin da sojojin ke amfani da su, wasu ma su na bukatar sai an yi masu garambawul tukunna.

Sojojin sun ce duk da irin tulin kudaden da ake cewa ana kashewa wajen yaki da Boko Haram ana sayo makamai na zamani, su dai ba su gani da idon su ba, sai tulin tsoffin kayan fama ake kai musu kawai.

“Irin wadannan makamai kuwa ba ma za ka iya jimirin yaki da Boko Haram da su ba.”

A cikin bidiyon kuma an ji su na cawa kwamandojin soja na amfani da su sun a samun kudade, ta hanyar ba su tankokin yakin da tuni lokacin amfani da su ya wuce.

Har ila yau kuma sojojin sun ce abokan yakin su sojoji da Boko Haram suka kashe, duk an kwace bindigogin su da albarusan da ke hannun su.

GUNA-GUNIN HASALALLUN SOJOJI

An rika jin guna-gunin hasalallun sojoji a cikin bidiyon su na bayyana yadda aka kashe sojoji ‘yan uwan su a wurin harin da Boko Haram suka shammace su.

“Mu ne sojojin Najeriya da aka kawo aka tula aka jibge mu a tsakiyar dokar dajin sahara. Jama’a ku dubi yadda hukumar sojan Najeriya ke wofintar da mu. Hari kawai ake kawo mana a wurin nan. Ku dubi yadda aka kone sojojin su a cikin motocin hilux. Su kuma kawai sun a mafani da mu ne suna tara makudan kudade. Saboda me ake yi mana haka? Shin mu ma ba mutane ba ne?”

Sojojin sun kuma ce Boko Haram sun kwashi manyan makaman sojojin Najeriya da suka hada da makaman harba rokoki na ‘40-Barell’.

“Ku dubi yadda suka lalata mana motocin yaki samfurin MRAP. To idan har makamin RPG na Boko Haram zai iya fasa MRAP, ya kuwa ba zai iya fasa jikin mu ba?”

An kuma rika nuno sojojin na bi dalla-dalla suna kidayar kayan fama da motocin sa aka lalata musu.

“Wannan tankar ce mayakan Albarnawy suka zo su lalata. Shin me ya sa ake amfani da mu su na yin kudi suna yin arziki ne? Mu na so gwamnatin tarayya ta sa baki kafin su bari dan ta’addan nan Albarnawy ya zo ya karkashe mu.”

“Gwamnatin Najeriya ta zo ta kawo mana gudummawa, su fa wadannan kwamandojin ce mana suke yi wai mu ba komai komai ba ne sai zombie, wadanda ba su san ‘yancin su ba. Amma bin da ba su sani ba, ai mu kwararrun sojojin zamani ne, ba sojojin bogi ba ne mu.”

“Mu fa ba irin sojojin 1963 ko 1979 ba ne. A cikin mu har masu digiri akwai fa.”

Sun yin ikirarin cewa su kan su wadannan tankokin samfurin T12 DA Boko Haram suka lalata, duk tsoffi ne, wadanda aka kera tun zamanin mulkin Shagari, cikin 1983 a kasar Slovakia.
“Bindigogi da manyan makamai ba su aiki sosai. Idan ka harba ratayen albarusai biyu, sai ka jira injin din ta ya yi sanyi tukunna kafin ta sake tashi. Kafin sannan kuwa ai Boko Haram sun shigo sun yi duk barnar da za su iya yi.

ILLAR MAKAMIN ‘40-Barrel’ A HANNUN DAN BOKO HARAM

Wani kwararren masanin muggan makamai, ya shaida wa PPREMIUM TIMES cewa makamin ’40-Barrel’, da aka fi sani da tashi-gari-barde, babbar barazana ce idan har ya fada a hannun dan Boko Haram.

Ya ce idan aka tsatstsage makamin da rokokin makami mai linzami, ana iya dura mata har 40. Sannan kuma a cikin sakan 20 zai iya cin nisan zangon kilomita masu yawan gaske. Sannan kuma shi barnar san a shafar wuri mai fadi ne sosai.

“Ni dai addu’a ta a nan, uku ce. Ko dai a kokarta sojojin mu su kwato wadannan makamai, ko kuma su gano daidai inda Boko Haram suka boye su, a je a kai hari a farfasa su, ko kuma kada Allah ya ba Boko Haram hikima da ilmin sani yadda za su iya sarrafa su.” Inji wannan kwararren masanin makaman yaki.

Share.

game da Author