Ba kamar Buhari, Ni dan kasuwa ne mai daukar mutane aiki – Atiku ga Buhari

0

Ofishin Kamfen na Atiku Abubakar ya bayyana cewa dan takarar su na shugabancin kasar nan a a karkashin jam’iyyar APC, mutum ne da ya dauki dubban jama’a aiki, su ke karuwa a karkashin sa.

Ofishin kamfen din ya yi wa Buhari gori da gwasalewar cewa Shugaban Kasa bai taba kafa wani kasuwancin da jama’a suka amfana da shi ba. Haka shi ma Sakataren Riko na APC, Yekini Nabena, ya dirar wa Atiku jim kadan bayan sanarwar cewa shi ne ya lashe zaben takarar jam’iyyar PDP.

“Mu yanzu mu na so ofishin Shugaban Kasa da kuma APC su lissafa mana kasuwanci daya tal wanda Buhari ya taba yi, har ya samu nasibin da jama’a suka amfana da shi. Mu na maganar saye da sayarwa, ba kiwon shanun sa guda 150 ba, wadanda har yau sun ki gaba sun ki baya tsawon shakara da sheakaru.”

Shekaran jiya Lahadi ne dai Daraktan Yada Labarai na Kamfen din Muhammadu Buhari, Festus Kiyamo ya rika yi wa Atiku tsokanar cewa ya gigice da neman mulki, har ta kai shi ga sayen kuri’un ‘yan takara.

Wannan ya sa ofishin kamfen na Atiku maida martanin cewa kowa ya ga yadda PDP ta gudanar da zaben fidda-gwanin da kowa ya yaba, ba kamar yadda na APC ya cika da rikita-rikita ba.

Sannan kuma ofishin ya nuna hatta zaben Buhari harkalla ce a zahiri, domin an tauye hakkin wasu ‘yan takara biyar, ba a tantance su ba, bayan sun rigaya sun sayi fam.

Sannan kuma ofishin ya tunatar da cewa hatta uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta jinjina cewa APC ta tafka rashin adalci.

A yau kuma ofishin na Atiku bai hakura ba, ya sake jefa makaman sa a kan Buhari, wanda suka tunatar da cewa kafin zaben 2015 ya ce, “Idan dai abin da aka yi a 2011 shi za a maimaita a 2015, to za a yi kare-jini-biri-jini”. Ofishin ya ce shi kuwa Atiku jan hankali ya rika yi a kan kaunar juna da zaman lafiya a lokacin.

“Yanzu dai ya rage wa ‘yan Najeriya su yi hukunci da kan su, domin ko makaho a hanzu ya san cewa Najeriya jina-jina ta ke da zubar da jini, tun daga lokacin da ta fada hannun shugaban da bai san komai ba, sai lalatarwa ba amfana wa kowa komai ba.

“Wawanci ne ma da sakataren APC a ce wai Atiku ya fadi abin da ya tsinana wa jama’a. amma dai a gare mu tambaya ce mai saukin amsawa, kamar yadda za mu ba shi amsa yanzu.

“Atiku Abubakar ya samar da ci gaba a Najeriya, domin a matsayin sa na Mataimakin Shugaban Kasa, shi ne shugaban kwamitin sayar da kadarorin gwamnati, ya yi sanadin shigo da wayar GSM a Najeriya. A da mutanen da ke da tarho ba su fi dubu amsin ba. Amma a yau sama mutane milyan 100 su na da tarho.

Atiku ya yi sanadiyyar karin samun gurabun aiki ga mutane sama da 500,000. Shi kuma Buhari mutum nawa ya samar wa aiki?

Ofishin ya kuma yi magana a kan yadda mulkin Buhari yaudari jama’a aka kafa sabon kamfanin jiragen sama da ofishin ya ce shirin duk na bogi ne.

Haka kuma ofishin ya tuna wa Sakataren APC, Yekini Nabena cewa baya ga kafa Jami’ar American University da Atiku ya yi a Yola, ya kuma kafa wani banki na bayar da lamuni, Microfinance Bank a Yola, inda mutane sama da 45,000 suka amfana.

Akwai kuma gandun kiwon dabbobin sa na Rica Gado, wanda ake amfana, kuma ya magance fadan makiyaya da manoma.

“Atiku ba zai taba dubar matasa ya ce musu ‘yan zaman kashe wando ba, domin rabin ma’aikatan sa kimanin 25,000 duk matasa ne.

A karshe sanarwar ta ce Atiku ne zai iya fitar da Najeriya daga kangin da ta ke ciki, inda matasa sama da miliyan 11 ba su da aikin yi.

Share.

game da Author