Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa daga yanzu fannin kiwon lafiya za ta yi amfani da kashi biyar daga cikin kashi daya na kudin da gwamnatin tarayya za ta ware wa fannin domin inganta bada tallafin gaggawa a kasar nan.
Ya fadi haka ne da yake zantawa da wasu baki daga kasar Britaniya da suka ziyarci Najeriya kan hada guiwa da hukumar hana yaduwar cututtukan na kasa (NCDC) domin inganta hanyoyin hana yaduwa da bulowar cututtuka a kasar nan.
Adewole ya ce za su fi maida karfi ne wajen hana yaduwa da bullowar cututtuka kamar su kwalara, monkey pox, sankarau, shan inna da sauran su sannan da kula da mutanen da suka yi hadari kuma ke bukatan kula na gaggawa.
” Fannin kiwon lafiyar ta amince ta horar da ma’aikatan mu kan amfani da dabarin zamanin wajen hana bullowar cututtuka sannan da yadda za a iya kula da mutanen da suka samu hadari cikin gaggawa.”
Discussion about this post