Hadiman Sanatoci da na Mambobin Tarayya sun yi zanga-zangar rashin biyan su Alawus-alawus

0

Wasu gungun hadiman ‘yan mahalisar tarayya sun gudanar da zangazangar lumana domin nuna rashin jin dadin kin biyan su hakkokin sun a kudaden alawus-alawus da ba a yi ba.

Sun gudanar da zangazangar ce a yau da safe yayin da Majalisar Tarayya ta koma aiki, bayan shafe makonni goma da aka yi ana hutu.

Sun rika rera wakoki yayin da suka samu wani gefe daya a cikin harabar ginin majalisar suka yi dandazo.

Kowanen su ya na dauke da kwalayen da aka yi wa rubutu, wanda a Hausance ke bada ma’anar cewa, “mu fa hadiman ku ne, ba bayin ku ba ne.”

Dama kuma ana sa ran cewa Majalisar Dattawa da ta Wakilai duk za su koma aiki a yau Talata.

Majalisar Dattawa ba ta yi wata-wata ba, nan da nan ta shiga taron daga su sai su kadai, wanda Shugaban Majalisar Dattawa0, Bukola Saraki ya jagoranta da kan sa.

Nyakari-Abasi Etuk ne ya jagoranci zangazangar lumanar, kuma ya shaida wa manema labarai cewa tun da Majalisa ta fara zaman ta na 2015, har yau ba a taba biyan su Kudin Alawus na Rangadi ba, da kuma sauran alawus-alawus ba daya ba.

“Tilas ta sa mun rika cin bashi a tsakanin junan mu, har ta kai wasu na bin wasu bashin milyan daya da wani abu. Kuma kudade ne da akan aike mu yin wani abu.

“Majalisar da ta gabata ta rika biyan mu dukkan hakkokin mu. Ba mu na ma magana ne akan a rika ba mu horo ba, wanda a cikin doka akwai yin hakan. Domin kamata ya yi a cikin shekara daya a rika ba mu horo na makamar aiki har sau hudu a shekara.

“Amma tun da muka fara a karkashin wannan gwamnatin, ba a taba ba mu horon sanin makamar aiki ba. Wanda muka yi a baya Hukumar Kula Da Majalisar Tarayya ce ta dauki nauyin gudanar da shi, ba majalisar da kan ta ba. Amma mu yanzu abin da muka fi damuwa da shi, a biya mu hakkokin mu kawai.” Inji shi.

“Wannan babbar matsala ce da ta shafe mu, domin mu na shaida wa kowa cewa ga shi dai an dawo daga hutu yau, amma wasu hadiman sun mutu, wasu kuma ko kudin biya wa yaran su kudin makaranta ya gagare su.

Ya ce a kowace shekara ana bada kudin alawus na hadiman majalisa a cikin kasafin kudade, amma sama da shekara uku ba a ba su ko sisi ba.

Ya ce hadiman da ke aiki a majalisa sun kai 3,000.

Share.

game da Author