Ba mu yi mamakin ficewar Hafiz Abubakar daga APC ba – gwamnatin Kano

0

A yau Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ficewar tsohon mataimakin gwamnan jihar Hafiz Abubakar daga jam’iyyar APC zuwa PDP abu ne da ya kamata ya faru tun tuni ba yanzu ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya sanar da haka wa manema labarai inda ya kara da cewa sun yi ta jiran haka tun ba yanzu ba.

” Muna da masaniyar cin amana da farfesa Abubakar ya yi a gidan taron Mambayya inda ya bayyan wa duniya cewa zai fice daga jam’iyyr APC duk da cewa ya yi shekaru uku yana rike da mukamin mataimakin gwamna da kwamishanan ilimi na jihar Kano.

Garba yace ficewar Abubakar daga gwamnatin jihar Kano ya nuna baude wa son yi wa talakawa aiki da shi Abubakar ya yi alkawarin yi tun farko.

A karshe Garba yace gwamnatin jihar Kano na yi wa Abubakar fatan alheri a harkokin siyasar sa da kuma mara wa sanata Rabi’u Musa Kwankwaso baya da ya sa a gaba ganin cewa su a wurin su hakan da ya yi arziki ne a gare su.

Share.

game da Author