Matasan Najeriya za su iya jan akalar makomar zaben 2019 – Shugaban INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya bayyana cewa idan idan matasa suka yi amfani da dimbin yawan da suke da shi har suka fito suka jefa kuri’a a zaben 2019, to kuri’un na su za su iya tantance wadanda za su yi nasara a zabukan.

Ya kuma bayyana cewa zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a ranar 22 Ga Satumba, zai kasance zaben gwamna mafi yawan ‘yan takara a tarihin zaben Najeriya.

Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke jawabi a taron Jami’an Gudanarwar Jami’ar Bayero da ta dauki nauyin shirin wayar wa matasa kai dangane da muhimmancin jefa kuri’a.

Yakubu ya ce tun daga yawan matasan da aka yi wa rajista, kuma suka karbi katin yin rajista tare kuma da yawan su da suka shiga zaben 2019, hakan ya nuna irin yawan da matasan da kuma tasirin su ke da shi a zaben Najeriya.

Daga nan ya ce daga lokacin da aka fara sabunta rajista cikin Afrilu, 2017 zuwa yau, an yi wa mutane kusan miliyan 11 rajista.

“Idan mu ka hada masu rajista tun tuni su milyan 70, zuwa lokacin da za mu shiga zaben 2019, zai kasance akwai masu rajista kamar milyan 80 kenan.”

Saboda haka mun zo a nan Jami’ar Bayero domin mu kara wa matsa kwarin gwiwa. Kuma mun rigaya mun ambaci ranar da za a rufe yin rajista, wato 17 Ga Agusta. Domin tun a ranar 27 Ga Afrilu, 2017 muke yin rajista.

Dangane da zaben gwamnan jihar Osun, Yakubu ya ce jama’iyyu 48 ne suka shiga takara, kuma shi ne zaben da ya fi kowane zabe yawan ‘yan takara a tarihin zaben Najeriya.

Ya ce zaben gwamnan jihar Ekiti da ya gabata kwanan baya, an samu ‘yan takara 37.

Share.

game da Author