Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya kori wasu kwamishinonin sa biyu da suka tarbi tsohon gwamnan, Godswill Akpabio, wanda ya koma APC.
Victor Antai na Al’adu da Shakatawa da kuma Ibanga Akpabio na Kwadago sun je har filin jirgin sama sun tarbi tsohon gwamnan.
Magoya bayan Akpabio sun cika filin jirgin domin yi masa lale marhabin.
Wata sanarwa da Sakataren Gwanatin Akwa Ibom ta fitar a yammacin Talata, wadda Emmanuel Ekuwem ya sa wa hannu, ta ce an salami Antai da Apbabio daga aiki saboda kin bin umarnin su na aiki da ka’idojin gwamnatin jihar.
Sanarwar ta umarci kwamishinonin biyu da su mika mulki ga manyan sakatarorin ma’aikatun su kafin lokacin tashi aiki a yau Laraba.
An samu wasu daidaikun ‘yan majalisar tarayya na Akwa Ibom da suka je tarbar Sanata Akpabio.
A yau ne za a yi masa wankan shiga APC a wani gangamin da za a gudanar a Ikot Ekpene.