Idan aka zabe ni shugaban kasa zan sauya fasalin Najeriya – Makarfi

0

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi ya bayyana cewa tabbas idan har ya zama shugaban kasar nan zai canza fasalin Najeriya.

Makarfi ya yi wannan furuci ne a garin Asaba, hedikwatar jihar Delta yayin da ya kai ziyarar ganawa da neman amincewar wakilan jam’iyyar sa ya zama dan takarar jam’iyyar.

Makarfi ya ce tabbas babban abin da zai fi maida hankali a kai shine sauya fasalin kasa Najeriya, cewa za a ba kowani yanki a kasar nan dama ta yadda ba za a sami wani bangare da zai na korafin ana muzguna masa ba ko kuma nuna masa wariya.

Ya roki wakilan jam’iyyar da su tabbata sun zabi dan takarar da zai fidda jam’iyyar daga kunya.

” Idan har muka yi abin da ya dace a matsayin mu na masu kishi da sanin ya kamata a PDP, ba mu bukatar sai mun kashe makudan kudade kafin mu yi nasara a zabe, da kadan din da muke da shi za mu iya yin nasara.

” Allah ne ya san gobe, mu dai namu shi ne mu tabbata mun yi zabe cikin adalci da gaskiya, banda karfa-karfa.

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya jinjina wa Makarfi sannan ya ce tabbas dan takara ne da ya san halin da kasa ke ciki, sannan kuma mutum ne da ke da gaskiya a al’amurran sa.

Share.

game da Author