Abin da Saraki da Obasanjo suka tattauna a asirce

0

A yammacin Litinin ne shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a garin Abeokuta jihar Ogun.

Saraki ya bayyana cewa ya ziyarci Obasanjo domin ya rangadin katafaren dakin karatun Obasanjon ne.

” Ko da aka kaddamar da dakin karatun ban sami damar ziyartar dakin ba shine yanzu na yi tattaki na musamman domin in ziyar ce dakin.” Inji Saraki.

Idan ba a manta ba a cikin makon da ya wuce, Saraki ya ziyarci garin Minna, inda ya kai wa Tsaohon Shugaban Kasa, Ibrahim Babangida ziyara.

Ana zaton ganawar ta su ba ta rasa nasaba da zaben 2O19.

Ganin cewa Saraki ya fice daga APC, ana hangen kuma Babangida da Obasanjo duk za su goya wa abokin adawar Shugaba Buhari ne baya a zaben 2019.

Share.

game da Author