Hukumar Zabe ta mika wa zababbun sanatocin Katsina da Bauchi Satifiket

0

Hukumar Zabe mai zaman kanta INEC ta mika wa zababbun sanatocin shiyyar Daura jihar Katsina da sanatan shiyyar Bauchi ta Kudu Satifiket.

Ahmad Babba-Kaita na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar sanata na shiyyar Daura, inda ya doke babban wan sa na jam’iyyar PDP, Kabiru Babba-Kaita.

A jihar Bauchi Lawal Gumau na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar sanata da aka yi.

Lawal ya doke tsohon shugaban gidan radiyon tarayya, Ladan Salihu na jam’iyyar PDP, da tsohon gwamnan jihar Isah Yuguda na jam’iyyar GNP.

Dukkan sabbin sanatocin da dama mambobi ne a majalisar wakilai ta tarayya sun yaba da yadda aka gudanar da zabukan a jihohin su.

Sai dai kuma jam’iyyar PDP musamman a jihar Bauchi ta yi tir da yadda aka gudanar da zaben a jihar.

PDP tace an hada baki da jami’an tsaro da wasu daga cikin ma’aikatan zabe wajen shirya magudi a zaben.

Jam’iyyar ta yi zargin yin amfani da kudi wajen siyan masu zabe.

Share.

game da Author