Yadda muka shigo da Buhari siyasa ya ci amanar mu – Buba Galadima

0

Wannan tsakure ne daga tattaunawar da Buba Galadima ya yi da PREMIUM TIMES.

“A shekaru 16 da muka yi na gwagwarmayar tafiyar Buhari, muna da daftari da kudirorin da muka tanadar domin ci gaban kasar nan. Musamman kan tsaro, tattalin arziki, matsalar matasa masu aikata laifuka musammam Boko Haram.

“Mun amince mu sa Buhari a gaba domin shawo kan wannan matsaloli saboda ganin cewa tsohon soja ne, ya na da kwarewar hakan kuma ba zai zama wata wahala a gare shi ba.

“Amma ya na cin zabe sai ya zama tamkar wani sarkin mulkin mallaka, ya kankane mulki shi da iyalin sa. Sai ya dauka cewa ko ba ministoci ma zai iya aiki, domin shi a ganin sa farin jinin sa ne kawai ya kai shi ga nasara ba kokarin wasu ba.

“Sai da ya ga mun jajirce mu na bude masa wuta sannan ya nada ministoci amma ba da son ran sa ba.

“Idan kun tuna a lokacin ai ya rika cewa ‘yan siyasa surutai kawai suka iya. Ba wanda ya san da mu ya ke yi don muna cewa ya kamata ya nada ministoci.

“Da ya zo nada ministocin sai ya kwaso har da wasu ma da ko takamaimen adireshin wurin zaman da za a iya samun su, idan an tashi neman su, ba su da shi. San nan kuma ya kwaso har da ‘yan-ta-more, wadanda ba da su aka yi gwagwarmaya ba.

“A yanzu da ya ke mulkin ai ga shi kowa na ji a jikin sa. Ga matsalar tattalin arziki. Ga rashin aikin yi kuma ga rashin tsaro. Mutane da yawa tsoron zuwa gona suke yi.

“Abin takaici kuma jama’a sun rasa ma inda za su fadi damuwar su. Saboda wannan gwamnatin ta dauki sojojin-baka sama da 300 a soshiyal midiya. Da zarar ka fito ka bayyana ra’ayin da ya saba ko ka fadi wani kuskure, to sojojin-bakan nan sai sun keta maka mutunci, ko kai wane ne.

“Babu ruwan wadannan sojojin-baka da yin nazarin maganar ka, aikin su kawai su shiga soshiyal midiya su tozarta ka.

“Ni na fara kiran wani taro a Kaduna gidan Bashir Dalhatu, wanda surukin Abacha ne. Akwai ni da Bashir Dalhatu sai Wada Nas da Sule Yahaya Hamma. Mu dai 34 ne muka taru muka tattauna yadda Obasanjo ke cin zarafin iyalin Abacha a lokacin. To daga nan ne batun shigo da Buhari cikin siyasa ya taso.

“To ya zuwa lokacin da aka rantsar da shi ba ya tare da ko mutum daya daga cikin mu 34 din nan. Duk ya zubar da mu, ya watsar da mu.

“Kai a ranar da za a rantsar da shi ma umarni ya bayar cewa kada a bar kowanen mu ya halarci bikin rantsarwar.

“A yanzu ya debo wadanda suka rika adawa da gaba da shi muraran a lokacin da mu ke tare da shi. Kuma wadanda ya tarkato din nan sure ne fa suka rika daure mu saboda mu na tare da Buhari.

“Cikin masu ikirarin masoyan Buhari na gaskiya a yanzu, har akwai wanda ya san mun san cewa su ne suka zauna a cikin daki a otal din Hilton suka rubuta sakamakon zaben 2007.”

“Shin bari na tambayi masu cewa don Buhari bai ba ni mukami ba na ke sukar sa. To a na su adalcin su na ganin bai kamata Buhari ya ba mu mukami ba?

“Wanda ke ganin Buhari ya yi daidai sai ya je ya yi wa wani bautar shekara 16 su na neman abu daya. Bayan ya samu sai ya watsar da shi sannan zai san amsar.

“Yau dai bari na maida wa Sanata Abdullahi Adamu raddin sukar R-APC da ya ke yi har ya na ce mana makiyan Buhari. Shi ne fa lokacin da ya na gwamnan jihar Nasarawa ya hana Sarakunan Gargajiyar jihar karbar Buhari idan ya je fadar su.

“Abdullahi Adamu ne fa ya ce duk Sarkin da ya bari Buhari ya je fadar sa, to bakin rawanin sa. Amma yanzu sun ga Buhari ke mulki wai su ne masu kaunar Buhari – har ya na da bakin kiran mu makiya Buhari.

“Na san wadanda ci wa zarafi saboda Buhari kuma na san wadanda ya daure saboda Buhari. Mutumin nan sai ga shi ya koma ya na faduwa gaban sarakuna ya na kuka ya na rokon su hana Barista Mohammed Abdullahi tsayawa takarar sanata tare da shi – soboda ya san karon ba zai yi masa dadi ba.

“Kakaf a cikin gwamnatin Buhari idan banda ‘yan ACN ka fada min wanda ba gyauron PDP ba. Kashi 90 bisa 100 na ministocin Buhari ‘yan PDP ne.

“Yau duk wani wanda ya sha zagi a baya ana ce masa rubabbe, barawo, kazami, mai laifi duk sun yi hijira zuwa APC. Duk dan PDP da ke tsoron kamun EFCC sai ya koma APC ya yi bakam kuma a karbe shi hannu bibbiyu.

“Duk wanda ka ga har yanzu ya na cikin PDP bai koma APC ba, to tsarkakke ne ba shi da wani aibi. To mu irin su muke so su zo mu tafi tare. Amma APC ta karbi ‘yan PDP har da masu tambarin garkuwa da mutane da kuma Boko Haram.

“Wa ya ce ba a sata a yanzu? Sun bar mulki mun hau ne mun fallasa su kun gani?

Karanta hirar a shafin mu na turanci: INTERVIEW: We brought Buhari into politics but he betrayed us – Buba Galadima

Share.

game da Author