OSUN 2018: Sanata, gwanin rawa, Adeleke ya zama dan takarar PDP a zaben gwamnan Osun

0

Sanata Adeleke ya ci zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Osun.

Adeleke ya samu kuri’u 1,569, yayin da mai bi masa Akin Ogunbiyi ya samu kuri’u 1,562, wato da kwaya bakwai kacal Adeleke ya yi rinjaye kenan.

Wasu sun nemi a sake lissafawa, amma sai shugaban shirya zaben, kuma Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson ya ce tunda ya rigaya ya bayyana sakamako, maganar sake lissafa kuri’u ba ta taso ba.

Adeleke tsohon dan APC ne, amma lokacin da yayan sa Isiaka Adeleke ya rasu sadda ya na Sanatan Osun ta Yamma, sai Adeleke ya canja sheka lokaci guda, ya tsaya takara a karkashin PDP kuma ya yi nasara.

Shi ne sanatan nan da ba ya gajiya da rawa ko a gaban wa takawa ya ke yi.

Share.

game da Author